Khalid Idris Doya" />

Rundunar Soja Ta Karyata Zargin Nuna Son Kai A Yayin Horar Da Sabbin Sojoji

Rundunar sojojin Nijeriya a jiya ne take karyata rahoton da ke bazuwa na cewar suna nuna banbanci da wariya gami da nuna ‘yan ubanci ga wasu bangarori a yayin horar da sabbin sojoji wanda ke ci gaba da gudunawa a sassan kasar nan a halin yanzu.

Babban Darakta a sashin hulda da jama’a na rundunar sojin Nijeriya, Bigediya Janaral Tedas Chukwu shi ne ya karyata hakan a cikin sanar’war da ya mallakar wa manema labaru, ya kara da cewa, rundunar sojojin Nijeriya ba ta taba shigar da kanta cikin harkokin siyasa, a kowani lokaci tana maida hankulanta ne kacokam wajen bin dokarsu da kuma ka’idojin da aikinsu a kowani lokaci.

Ya nunar da cewar babu wata jiha a fadin kasar nan, ciki kuwa har da jihar Adamawa da wani abu makamancin wannan ya auku kamar yadda ake zarginsu a cikin rahoton da aka fitar din ta kafafen sadarwar zamani.

Sanarwar ta yi bayanin cewar “Rundunar sojin Nijeriya tana son ta warware batun wannan zargin wanda a cikinsa kwata-kwata babu kamshin gaskiya ko kadan a ciki, bi-hasalima labari ne kawai marar makama da tushe,”

Bigediya Janaral Tedas Chukwu ya kara da cewa, “wannan aikin na wasu ne kawai marasa kishi da a kowani lokaci burinsu su ga sun bata wa rundunar sojinmu suna da irin wannan kagen nasu,”

“Maganar gaskiya a tarihin daukan masu samun horon shiga soja, muna bin hanyoyin da suka dace ta hanyar amsar takardun da suka dace ga kowani mai sha’awa, da zarar mutum ya cike sharadi kuma za mu bashi damar fitowa ya fafata neman sa’a,”

Ya kuma daura da cewa, “Dukkanin wadanda suke neman wannan damar ta shiga soja da suke amsar horo a Demsa, Numan, Lamurde da kuma karamar hukumar Girei a yanzu haka suna ci gaba da amsar horarwa kamar kowani mai bukatar shiga soji a wannan lokacin,” In ji Tedas.

 

Exit mobile version