Umar A Hunkuyi" />

Rundunar Soja Ta Sanar Da Sabbin Mukamai Da Karin Girma

A jiya ne, rundunar Sojin kasar nan ta sanar da canje-canjen wuraren aiki da kuma sabbin nade-nade ga wasu manyan jami’anta.
Sanarwar wacce ta fito daga Kakakin rundunar, Kanar Sagir Musa, tana cewa, a ranar 16 ga watan Mayu, 2019 ne rundunar Sojin ta fitar da sabbin nade-naden.
Ya ce, wadanda abin ya shafa sun hada da Manjo Janar H. O. Otiki, wanda aka yi masa canjin wurin aiki zuwa bataliya ta 8 da ke Sakkwato, a matsayin babban Kwamandan bataliyar (GOC).
Manjo Janar S.O. Olabanji, na batalya ta 8, yanzun an mayar da shi sashen, Infantry Corps Centre a matsayin babban Kwamanda.
Birgediya Janar H.I. Bature, yanzun ya koma shalkwatar bataliya ta 34 a matsayin babban daraktan gudanar da jarabawa da kuma Birgediya Janar T.O. Olowomeye, wanda aka dauke daga bataliya ta 33 zuwa,’ Army Headkuarters Department of Cibil-Military Affairs, a matsayin babban daraktan, Cibil Military Affairs.
Hakanan, Birgediya Janar B.A. Mohammed, yanzun an dauke shi daga bataliya ta 23, zuwa Martin Luther Agwai International Peace Keeping Centre, a matsayin mataimakin Kwamanda. Shi kuma Birgediya Janar U.M. Bello, an dauke shi daga shalkwatar bayar da horo, zuwa bataliya ta 63 Brigade, a matsayin Kwamanda.
Shi kuma, Birgediya Janar B.A. Mohammed, yanzun an dauke shi daga bataliya ta 23 Brigade, zuwa, Martin Luther Agwai International Peace Keeping Centre, a matsayin mataimakin Kwamanda, shi kuwa Bigediya Janar U.M. Bello, an dauke shi ne daga shalkwatar, Training and Doctrine Command, zuwa bataliya ta 63 Brigade a matsayin Kwamanda.
Birgediya Janar M.T. Durowaiye, daga Directorate of Army Transformation and Innobation, yanzun an mayar da shi bataliya ta 33 Brigade, a matsayin mataimakin Kwamanda.
Sauran su ne, Birgediya Janar S.B. Kumapayi, daga, Army Headkuarters Department of Cibil-Military Affairs, zuwa shalkwatar bataliya ta 14 Brigade, a matsayin Kwamanda, sai kuma, Birgediya Janar N.M. Jega, daga shalkwatar bataliya ta 2 Brigade, zuwa bataliya ta 9 Brigade, a matsayin Kwamanda.
A sauyin da aka yi na kwana-kwanan nan, Birgediya Janar K.O. Aligbe, Kwamandan, Birged ta 16, yanzun an mayar da shi shalkwatar tsaro a matsayin mukaddashin daraktan hulda da majalisun kasa.
Birgediya Janar A.K. Ibrahim, yanzun an dauke shi daga Birged ta 14, zuwa, Army Headkuarters Department of Administration, a matsayin mataimakin Darakta, Beteran Affairs Department Retired Officers’ Cell, sai Birgediya Janar G.T.O. Ajetunmobi, wanda aka dauke daga shalkwatar tsaro, Army Records, zuwa Birged ta 31, a matsayin Kwamanda. K.O. Aligbe, Kwamandan Birged ta, 16, yanzun an mayar da shi, Defence Headkuarters, a matsayin mukaddashin daraktan hulda da majalisun kasa.
Birgediya Janar O.G. Onubogu, shi ma an dauke shi daga shalkwatar Sojojin zuwa shalkwatar Birged ta 16, a matsayin Kwamanda, shi kuma, Birgediya Janar O.M. Bello, yanzun an dauke shi daga Nigerian Army Resource Center, zuwa shalkwatar bataliya ta 6, a matsayin shugaban ma’aiakata.
Birgediya Janar Z.L. Abubakar,an dauke shi daga, National Defence College, zuwa Birged ta, 32, a matsayin Kwamanda, sai Birgediya Janar A.A. Orukotan, daga Nigerian Army Resource Center, zuwa shalkwatar, Headkuarters Command Army Records, a matsayin shugaban ma’aikata.

Exit mobile version