Connect with us

LABARAI

Rundunar Soja Ta Yi Bayani Kan Bacewar Manjo Janar Alkali

Published

on

Rundunar sojojin Nijeriya ta kalubalanci wata kungiyar kasar Birtaniya mai suna ‘Citizens United for Peace and Security (CUPS)’ wadda Dakta Idris Ahmed ke yi wa shugabanci da ta fito da bayanan dake nuna cewa, rundunar bata damu da bacewar hafsan sojanta Manjo Janar Idris Alkali, ko kuma su dai na wasa da sanya siyasa a da lamarin rayuwar hafsan sojan.

Daraktan watsa labaran rundunar sojan ta kasa, Birgediya janar Tedas Chukwu, ya bayyana haka a wata takardar sanarwar da aka raba wa manema labarai a Abuja, ya ce, duk da harin da ake kai wa rundunar, sun sha alwashin tabbatar da gani tare da warware al’amarin dake tattare da bacewar hafsan gaba daya.

“An jawo hankalin rundunar sojojin Nijeriya a kan mutane irinsu Idris Ahmed da kungiyoyinsa na kasar Birtaniya, a kan yadda suke nuna cewa, kamar rundunar sojojin bas u nuna damuwa ba a kan bacewar hafsan sojan da kuma cewa wai a kwai hadin baki a tsakanin rundunar sojojin a kan bacewar hafsan sojan baki daya. A saboda haka rundunar sojojin Nijeriya na son bayyana cewa, “Manjo Janar IM Alkali (N/8353) ya yi murabus daga aikin soja a ranar 7 ga watan Agusta 2018 bayan ya yi aiki tukuru na shekara 35 da wata daya da kwanaki 3 a gidan soja na kuma kare kasarsa ta haihuwa,’ inji shi.

Rundunar sojan ta kuma bayyana cewa, Manjo Janar IM Alkali ya yi murabus ne a matsayin Babban Hafsan soja a saboda haka yana da alfarmar kasancewa tare da direbansa na soja da kuma wani hadiminsa, wadanda kuma suna tare da shi har zuwa lokacin daya bace.

Sanarwa ta kuma ce, shugaban rundunar Sojojin Nijeriya Janar Tukur Burutai ya bayar da umurnin yin duk abin daya kamata don gano da kuma kubutar da Hafsan Sojan da gagawa.

A kan cewa, Rundunar Sojan na da hannun a kan bacewarsa kuma bamu nuna damuwa ba, wannan karya ne kuma kamar wasa yara ne gaba daya, bai kuma yi kama da gaskiya ba.

“Muna kirab ga Dakta Idris Ahmed day a kawo hujjojin wannan zargin nasa, nuna kuma bas hi shawarar ya kauracewa sanya siyasa a batun rayuwar mutum.

“Mna sanar da Dakta Idris Ahmed daya koma ga masu daukar nauyinsa cewa, bai samu nasarar bata sunan shugaban rundunar sojojin Nijeriya Laftanar Janar TY Buratai tare da rundunar sojojin Nijeriya baki daya.

“Kasancewar baban hafsan sojan nIjeriya mai ritaya Manjo Janar IM Alkali na da ikon zirga zirga tafiya a dukkan fadin kasar nan ba tare da neman izinin rundunar sojan Nijeriya ba,”

Sanarwa ya kuma ci gaba da cewa, Manjo Janar Alkali na da ikon tafiya duk in da yake so tare da direbans ko ba tare da direbansa ba, sun kuma kara da cewa, a ranar 5 ga watan Satumba 2018 ne mata hafsan mai suna Misis Salamatu Alkali ta jawo hankalin rundunar sojan Nijeriya a kan bacewar babban hafsan.

“Bayanin da matar hafsan sojan  ta yi ya nuna cewa, mijin nata ya bar gida ne a ranar 3 ga watan Satumba 2018 daga gidansu na Abuja zuwa Bauchi.

“bayanin ya nuna cewa, hafsan ya yi tafiyar ne ba tare da Direba bad a kuma hadiminsa, ya kuma tuka kansa ne a mota kirar Toyota Corrolla mai launin baka.

“matar ta kuma yi bayanin cewa, ta yi Magana da mijin nata ne ta lambar wayarsa ba 09056890335, in d ace mata, ya wuce garin Jos yana kan hanyarsa ta zuwa Bauchi.

“bayan jin wannan rahoton ne rundunar sojoji Nijeriya ta sanya masu, jami’in soja daga rundunar leken asiri don ya zama jakada a tsakanin iyalan da rundunar sojojin, an shiya kuma jami’in ya taumaka wajen samun cikkakne bayanan da za a yi amfani das u daga iyalan don ci gaba da bincike da ake yin a gano inda hafsan sojan yake.

“Rundunar sojan ta kuma tuntubi hukumar sadarwa ta MTN da Glo don samun dukkan bayan kiraye kirayen da hafsan ya yi da wayarsa.

“wannan bayan da aka samu daga hukumar sadarwa ta MTN da GLO suka taimaka wajen gano motsi wayar a wani yanki da ake kira Du kusa da garin Jos ta jihar Filato.

“Shugaban rundunar sojojin Nijeriya COAS ya umurci Kwamanda rundunar ‘Operation Safe Haben’ da shugaban runduna ta  3 da sauran jami’an tsaro su hada hannu don gano hafsan Soja.

“A yayin gudanar da bincike ne a ka fahinci yiwuwar cewar an kashe shi tare da jefa gwarsa a waani kududdupi tare da motarsa a yankin na Du dake a karamar hukumar jos ta Kudu.

“Tun da rahoton bacewar hafsan ya bayyana, shugaban sojoji Nijeriya ya umurci a tabbatar da yin dukkan abin daya kamata na ganin an ceto hafsan soja.

“duk da kokarin kawar da hankalin sojan Nijeriya a kan aikin ceto hafsan da wasu mata tare da wasu masu ikirarin neman yanci, sojan Nijeriya ta sha alwashin gano gasukiyar lamarin gada daya.

“Ya zuwa yanzu a na kwafe kududufin don sojojinmu su ga me ke a ciki gaba daya,”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: