Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola
Rundunar sojan saman Najeriya na kashe sama da naira miliyan Dari uku da arba’in da hudu da dubu dari hudu da hamsin da biyu (N344,452,630) wajan kai hari kan sansanonin kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin kasar.
Shugaban rundunar Operation Lafiya Dole Air Commander Tajujdeen Yusuf ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da rundunar ke gudanar bayan kowane wata uku, rundunar kan kashe wadannan kudaden wajan kai hare-hare a sansanonin kungiyar boko haram.
Shugaban rundunar samar da zaman lafiya a yankin ya ci gaba da cewa rundunar na kashe naira miliyan 343,700,56 wajan kudin man jirgin yaki lamba daya, haka kuma rundunar na kashe naira miliyan 1,751,070 wajan samar da man gas domin kula da jiragen.
Haka kuma rundunar ta bayyana matsalar yanayi da cewa shine babban kalubalen da take fuskanta wajan kai hari kan mayakan kungiyar boko haram,yace lamarin na baiwa yan ta’addan boko haram daman sulalewa da kaucewa hare-haren rundunar akan wuraren da dama ta tsara zatakai harin.
Da yake magana game nasarorin da rundunar ta samu cikin watanni uku kuwa Air Commode Tajujdeen Yusuf, yace rundunar ta samar da tallafin jinkai da jinyar kyauta ga ‘yan gudun hijira 201, da wasu marasa 133 lafiya da’aka yiwa aiki, yace akwai kuma wasu 68 da’aka yiwa aiki akan wasu cututtuka daban daban.
Ya ce akwai mata 40 daga sansanonin ‘yan gudun hijira daban daban da’aka yiwa aikin cutar kansa, tace ta kuma kwashe yan matan chibok 82 daga Banki zuwa Maiduguri kafin a tafi dasu fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Haka kuma rundunar ta tabbatarwa ‘yan Najeriya da alumman yankin arewa maso gabas samun tabbataccen zaman lafiya a yankin.