Rundunar Soji Ta Kashe Mayakan Boko Haram 15 A Jihar Borno

Rundunar soja ta Bataliya 242 tare da hadin guiwar rundunar soji ta MNJTF da kuma rundunar sojin kasar Chadi ta CDF sun kashe mayakan Boko Haram goma sha biyar a jihar Borno.

Kanal Aminu Iliyasu, Jami’in watsa labarai na rundunar sojin shi ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.

Iliyasu ya ce; rundunar sojin ta hadin guiwa sun dakile harin ‘yan ta’addan Boko Haram din ne a kauyen Jigalta a ranar Alhamis a daidai Marari kilomita 27 da garin Mongunu na jihar.

Ya tabbatar da cewa mayakan Boko Haram din ne da ba a kai ga tantance adadinsu ba suka kai harin farmaki ga rundunar sojin, da muggan makamai. A cewarsa, sun yi nasarar hallaka mayakan Boko Haram din 15 tare da dakile harin su, inda wadansu da dama suka tsira da raunuka.

Sannan ya ce ba ya ga haka sun yi nasarar tarwatsa muggan motocin makaman na su da suka kawo musu hari da shi.

Exit mobile version