Kwamandan Rundunar, ‘Operation Lafiya Dole,’ rundunar da ke fafatawa da ‘yan ta’adda a yankunan Arewa maso gabashin kasarnan, ya karyata rahotannin da ke nu ni da bacewar Sojojin rundunar 23 gami da manyan motocin rundunar 8.
Manjo Janar Nicholas Rogers, ya shaida wa gidan talabijin na ‘Channels,’ ranar Litinin cewa, sam babu ma wani rahoton yi wa rundunar wani kwantan bauna, Sojojin dai suna gudanar da ayyukansu ne kamar yadda suka saba a yankunan na Kwakwa da Bula Naglin, na Jihar ta Borno.
Ya bayyana cewa, a lokacin da suke gudanar da aikin nasu ne wasu daga cikin motocin nasu suka gaza saboda rashin kyawun hanya, wanda a lokacin ne ‘yan ta’addan suka kawo wa Sojojin hare-hare har sau biyu, kuma duk Sojojin suna kora su tare da agajin mayakan Sojin ta sama.
Ya bayyana cewa a hakan ne aka ji wa wani babban jami’in rundunar da kuma wani Soja guda ciwo, amma sun kashe sama da maharan ‘yan ta’addan na Boko Haran 22 a lokacin fafatawan. Yayin kuma da aka kwaso motocin da suka gazan aka kuma kai karin dakarun Soji.
A karshen mako ne dai wasu kafafen yada labarai suka watsa rahotannin da ke cewa, akalla Sojin Nijeriya 23 ne suka bata, bayan wani kwantan bauna da maharan ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi masu a kauyan Boboshe, da ke karamar hukumar Bama, ta Jihar Borno.
Aka ce kuma takwas daga cikin manyan motocin sojan 11 da aka tura domin su kawar da ‘yan ta’addan sun bace bayan harin na kwantan bauna a ranar ta Asabar.