Abubakar Abba" />

Rundunar Sojin Sama Ta Cafke Masu Fasakaurin Dizil, Ta Qwace Durom 501

Rundunar Sojin sama dake jihar Akwa-Ibom ta yi bajin kolin mutane takwas data cafke bisa zargin fasakwarin Diram-Diram na Man Dizil na AGO guda 501.
Kwamandan mai rikon kwarya na rundunar FOB dake yaki da masu fasakaurin mai Kaftin Reginald Adoki ne ya sanar da hakan a ranar litinin data gabata a lokacin da yake mikawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa da kuma yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC wadanda ake zargin da kuma diram-diram din na man AGO da jirgin kwale-kwalen da suka yi fasakwarin dasu guda uku yankin Ibaka dake cikin jihar.
Acewar sa, rundunar ta samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayan data samu rahotom sirri akansu a ranar 5 ga watan Afirilun shekarar 2019 dauke da man da suka yo fasakaurin sa daga yankin Oyorokoto dake cikin jihar Ribas daura da garin Kalaba zuwa Oron a cikin kwale-kwale uku.
Kaftin Reginald Adoki ya ci gaba da cewa, a bisa binciken da suka gudanar, suna zargin an sarrafa man ne ta haramtacciyar hanya, inda ya yi nuni da cewa, tabbas daga alamun ayyukan wadanda ake zargin sun jima suna yiwa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta hanyar fasakauri.
Ya kara da cewa, cafke wadanda ake zargin da kuma mika su ga hukumar ta EFCC, hakan ya nuna a zahiri jami’an sa a shirye suke wajen magance ta’sar fasakaurin mai a jihar.
Kayan da kuma wadanda ake zargin Shugaban Shiyya na Hukumar EFCC dake Uyo Abdulkarim Chukkoh ne ya karbe su a madadin EFCC.
Xaya daga cikin wadanda ake zargin Victor Umana da ya fito daga karamar hukumar Mbo dake cikin jihar, Akwa Ibom ya bayyana cewa, ya shiga aikata fasakaurin ne saboda rashin aikin yi.

Exit mobile version