Rundunar Sojin Sama Ta Jaddada Aniyarta Na Kare Kasar Nan

Daga Bello Hamza,

Rundunar sojin sama (NAF) ta kara jaddada kudurinta na kare tarayyar kasar na daga duk wani hare hare daga ciki da kuma wajen kasar nan.

AVM Hassan Abubakar, shugahan kwamitn shirya taron cikar rundunar shekara 57 da kafuwa ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai.

Ya ce, rudunar soji saman Nijeriya ta gawurta a shekarun nan ta kuma yi karfin kare kasar nan daga duk wani barazana daga ciki da kuma kasashen waje.

Ya ce, rundunar ta gudanar da aiki a kasashen yankin Afirka ta yamma da dama in da ta samu gaggarumin nasarar ceto rayuwa da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma ce, taken wannan bikin shi ne ‘Enhancing Nigerian Air Force Airpower Capabilities for Effective Joint Operations in Response to Contemporary National Security Challenges’, an kuma zabo wannan taken ne don kara karfafa dakarun rundunar ta wajen fuskantar ayyukan kare kasar nan daga barazanar masu tayar da kayar baya a cikin kasar nan gaba daya.

Ya kuma kara da cewa, take ya kuma yi daidai da yadda shugaban rundunar sojin saman Air Marshal Oladayo Amao ya shirya ganin rundunar na kara mata karfin gudanar da ayyukanta tare da hadin kan dukkan sauran rundunonin tsarin kasar nan gaba daya.

“A bikin za a yi gasar wasa ga jirgi sama kirar L-39-ZA, A-JET da kuma JF-17, za kuma a gudanar da ayyukan jinkai a rundunar da ke bangarorin kasar nan, za kuma a bayar da talafin jinkai wadanda kungiyar matan manyan sojoin sama NAFOWA za ta gabatar a yankunan kasar nan gaba kaya.

“Haka kuma likitocin rundunar za su bayar da kulawa na kiwon lafiya ga al’ummma a barikokin rundunar da ke fadin tarayya kasar na, musamman da Abuja.

Za kuma a gabatar da taruka da za a gabatar da mukalolin da za su samar da mafita ga abuwan da kasar na ke fuskanta a halin yanzu.

Exit mobile version