Rundunar Sojin saman Nijeriya bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta sake yin wata barnar a kan masu tayar da kayar baya da ke addabar Arewa maso gabashin kasar nan, tare da kawar da ‘yan ta’addan da lalata motocin daukar bindigoginsu a Ajiri da ke Jihar Borno.
Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin m akon nan, a inda yake cewa, an cimma wannan nasarar ne a daren 19 ga Disambar, 2020, biyo bayan wasu rahotanni da aka samu da ke nuna cewa ‘yan ta’addar, a cikin manyan motocin bindiga 7 sun yi yunkurin keta Ajiri, wani matsuguni a karamar hukumar Mafa ta jihar.
Dangane da hakan ne rundunar sojin sama ta aika da wasu runduna ta jiragen sama masu saukar ungulu na rundunar Sojin sama (NAF) don fatattakar ‘yan ta’addan. Jirgin NAF din ya kawo cikakkun bayanai, a inda ya tarwatsa manyan motocin bindigogi 2 tare da kashe ‘yan ta’adda da dama.