Rundunar Sojin saman Nijeriya, bangaren dakarun ‘Operation LAFIYA DOLE’ ta sake yin wata barna a kan ‘yan ta’addan Boko Haram da ke addabar Arewa maso gabashin kasar, tare da lalata motocin bindigogin su da ba su gaza 3 ba, a inda suka rundunar kuma ta murkushe mayakansu da dama a Mainok da ke jihar Borno.
Jami’in yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu cikin makon nan, a inda yake cewa, an gudanar da harin jirgin ne a ranar, 12 ga Janairun 2021, sakamakon rahotannin sirri da ke nuna cewa ‘yan ta’addan a cikin manyan motocin bindiga suna bin hanyar Jakana-Mainok na jihar.
A bisa haka ne, rundunar ta binciko jiragen yaki masu saukar ungulu na NAF don tarwatsa ayarin motocin bindigogin nasu da na kayan aikinsu. Jirage masu saukar ungulu sun ba da cikakkun bayanai a yankin da aka nufa, wanda ya haifar da lalata motoci 3 na ‘yan ta’addan, a inda aka ga wasu daga motocin suna ci da wuta. Da yawa daga cikin ‘yan ta’addan an kuma kawar da su a yayin harin.
Sojojin Nijeriya ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai an kawar da dukkan makiyan al’umma, sannan an dawo da al’amuran yau da kullum a dukkan yankunan kasar da ke fama da rikici.