Rundunar Sojoji Na Taron Horar Da Jami’anta Karo Na 21 A Zamfara

Shugaban rundunar sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bude taron horarwa na sojoji a kan kimiya da inganta kiwon lafiya a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Shugaban Sojojin ya kuma bayyana cewa, “rundunar Sojojin Kasar nan , ta’kara kaimi wajan Kere – kere da kuma gine gine ,da tituna dan amfanar alumna da jami’an soja .

Gen. Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar rundunarsa zata cigaba da kare rayuwar al’ummar kasarnan daga dukkan nasu’ aikan taaddanci.

Shima anasa jawabin, shugaban fannin kerekere da kimiyya na rundunar sojin Nigeria, Major General JB Olawumi ya bayyana cewar an fara kaddamar da taron shekara shekara na bangarensa a shekarar 1989, yayin da yace ansamu cigaba ta fannin kerekere da fasahohi a tsakanin jamian sojin Nigeria a shekaru 21 dasuka gabata a kasarnan.

A jawabinsa Gwamnatin Jahar Zamfara yayi kira ga gwamnatin tarayya data tallafamata wajen Samar da ingantattun ababen more rayuwa ga al’ummar Fulani da gwamnatin jihar ke kokarin Samar wa Matsugunin dindindin a jihar a kokarinta na tabbatar da sasanci tsakanin Fulani da gwamnatin jahar.

Gwamna Matawalle ya ce, kiran ya zama dole, don ganin shirin zama lafiya a jihar ta hanyar sulhu ya dore tare da inganta rayuwar Fulani makiyaya da al’ummar jihar bakidaya.

Gwamna Matawalle ya jinjinawa sojojin Najeriya bisa jajircewarsu na tabbatar da kakkabe duk wani nau’in ta’addanci a fadin kasar.

Exit mobile version