Rundunar ‘Yan Sanda Ta Cafke Gawurtattun ‘Yan Fashi A Jigawa

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa, ta yi nararar cafke wadansu gawurtattun ‘yan fashi da suka addabi kauyukan dake garin Gwaram‎ a jihar ta Jigawa.

Kwamishinan ‘yan sanda reshen jihar CP Bala Zama Senchi ne ya bayyana haka ta hanyar kakakin rundunar SP Abdu Jinjiri a lokacin‎ da suke baje kolin ‘yan fashin a yammacin jiya a farfajiyar hedkwatar ‘yan sanda dake birnin Dutse.

CP Senchi ya ce, ‘yan fashin sun fado komar rundunar tasu bayanda suka cafke wani mai suna Sa’adu Sulaiman dake kauyen Yarfi a yankin a ranar ‎26/09/2018 wadda ake zarginsa da aikata fashin a yankunan.

Ya ce bayan da aka zurfafa bincike, wadda ake zargin ya amsa laifinsa gamida zayyana sauran gungun abokanan fashin nasa wadanda suka addabi wannan yanki.

Mai laifin ya bayyana sunayensu wadanda suka hadarda‎ Bature lawan, Isah Babba, Muh’d Shehu Alias Dunkule wadanda tuni suka fada komar ‘yan sandan.

Sannan kuma yace, sauran sun hadarda Malam Niga Ibrahim, Sale Kaduna, Yellow Nafara Mai unguwa dukkanninsu sun fito daga yankunan jihohin na Jigawa da Bauchi kuma tuni suka ranta a na kare.

Masu laifin sun bayyana cewa, sune da alhakin duk wani fashin da aka gudanar a yankin wadda a cewarsu suka hadarda.

Fashi a kauyen Ranbazau dake karamar hukumar ta Gwaram yadda suka a yi awon gaba da tsabar kudi har kimanin N975,000 da kuma yin Fashi a Garin Gwaram yadda suka kwace N150,000 da kuma sabon Babur kirar Bajaj sannan kuma da fashi a garin Sara yadda suka kwace tsabar kudi har naira milyan biyu daga hannun wani Inyamuri.

Kwamishinan ya kuma ce, a yayin bincike an same su da bidigogi guda biyu irin na gargajiya sannan kuma tuni rundunar tasu ta dukufa don zakulo sauran da suka gudu domin girbar abin da suka aikata gaban kuliya.

 

Exit mobile version