Daga Wakilinmu
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Legas ta kama Tabar Wiwi da kuma wasu mugayen ƙwayoyin masu tsada da aka ƙiyasta kuɗin su ya kai sama da naira miliyan 20.
An kama Tabar ce, a wani samame da ‘yan sanda suka kai a wata maɓoyar ɓata gari da ke unguwar Itire a Mushin, inda aka samu Tabar a cikin Buhunhuna 38.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Edgal Imohimi wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai ya ce, an kuma kama waɗanda ake zargi su 52 lokacin da aka kai samamen.
Edgal ya ƙara da cewa an samu wanna nasarar ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin rundunar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar alummar jihar da suke da ƙyaƙƙyawat alaƙa tun da daɗewa, mazauna yankin da abin ya auku ne suka sanar da jami’anmu wannan maɓoya ta ɓata garin.
Ya ci gaba da cewa, a bisa bayanan da muka samu, ɓata garin sun jima suna cin Karen su ba babbaka a yankin, suna aikata ta’asa, inda ya bada umarnin da akai samamen da daddare don kama ɓata garin har aka samu nasarar kama maza 44 da mata 8 tare da kuma buhun Tabar Wiwi 38.
Kwamishinan ya ce, an kuma kama waɗanda ake zargin da wasu mugayen ƙwayoyi da aka yi masu laƙabi da ‘’Bible’’, inda ya ja hankalin al’ummar jihar da su farga da irin waɗannan mugayen ƙwayoyi.
Sannan ya yi kira ga al’ummar jihar ta Legas da su sa ido akan mugayen ƙwayoyin don gudun kada a sayarwa ‘ya ‘yansu, saboda hakan na iya haifar da wasu illoli.
A cewar kwamishinan, ya lura da alaƙar da miyagun ƙwayoyi da yawan aikata manyan laifufuka yasa muka haɗa gwiwa tsakanin mu da Hukumar Hana Sha da fataucinmiyagun kwayoyi watau (NDLEA) da kuma sauran jami’an tsaro don yaki da shaye-shaye a ɗaukacin faɗin jihar Legas da kewaye.
Mista Edgal, ya bayyana jin daɗinsa akan haɗin kan da al’ummar jihar suke baiwa rundunar, kuma za su cigaba da yin iyakar ƙoƙarinsu don bankaɗo dukkkan maɓoyar ɓata gari da ke cikin jihar ta Legas.