Rundunar ‘Yan Sanda Ta Karawa Jami’anta 766 Girma A Kebbi

Rundunar ‘Tan sanda ta kasa reshen jihar kebbi ta gudanar da bukin Karin girma ga jami’anta 766 a rundunar ta jihar kebbi a jiya a Birnin-kebbi.

Taron bukin an gudanar da shine a hedkwatar rundunar ta ‘yan sand da ke a Birnin-kebbi a jiya.

Da yake gabatar da jawabinsa kafin soma bukin na karin girma ga jami’anta rundunar, kwamishina mai kula da rundunar ta jihar kebbi Alhaji Ibrahim M. Kabiru ya bayyana cewa a cikin kuduran insifeto janar na kasa Ibrahim Kpotun Idris shine ya tabbatar da walwala da jindadin jami’an rundunar ta ‘yan sandan kasar nan da kuma biyan su albashi a cikin lokaci, saboda haka ya karima jami’in rundunar jihar kebbi 766 girma Kama tun da ga makamin insifeto har zuwa ga Marar mukami a rundunar kawai ta jihar kebbi.

Jami’an da suka samu Karin girman sun had da masu mukamin sajan zuwa insifeto jami’i 181 da kuma kofurori zuwa mukamin sajan 585 duk a rundunar ta jihar kebbi.

Kwamishinan rundunar CP Ibrahim Kabiru ya ci gaba da cewa “karin girman anyi shine domin a karama jami’an ‘yan sanda kwarin gwiwa kan gudanar da aiki dansan a kasar nan”. Hakazalika ya yi amfani da wannan dama domin nuna jindadinsa da kuma godiyarsa ga jama’ar jihar kebbi kan irin taimako da kuma goyun baya da suke bayar wa wurin bada bayanan sirri ga jami’an rundunar ta ‘yan sandan jihar, domin bisa ga bayanan da a ke bayar wa ta hakan ne aka samu nasarori ga rundunar, inda jihar kebbi ta zama daya daga cikin jahohin da sukafi kowace jaha zaman lafiya da kuma harakar tsaro”.

Daga nan kwamishinan ya ja kunnuwa jami’an rundunar da su ci gaba da zama jakadu na gari a cikin aiki gidan dansanda a kasar nan da kuma gudanar da ayyukkaansu kamar yadda dokar aikin dansanda ya tanadar.

Taron bukin karin girman ya samu halartar dukkan DPO DPO da mataimakansa masu Kula da kananan hukumomi guda 21 da ke akwai a jihar ta kebbi da kuma sauran wasu manyan ‘yan sanda da ke a rundunar ta jihar kebbi.

 

Exit mobile version