A makon jiya ne rundunar ’yan sandar shiyyar karamar hukumar Makarfi da ke a jihar Kaduna ta yi nasarar kashe wasu ’yan fashi da makami guda biyu a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Wakilinmu ya ziyarci yankin da lamarin ya faru, don kawowa masu karatunmu gaskiyar lamarin kamar haka.
Bincike ya tabbatar da cewa babban titin hanyar Kano zuwa Zariya na cike da kalubale na matsin lamba daga ’yan Fashi wanda ya kan sa a na rasa rayuka lokaci bayan lokaci duk da kokarin da jami’an tsaron kan yi na zirga-zirga a hanyar, don kare rayukan jama’ar da ke bi hanyar.
Bisa haka ne wasu barayi masu karar kwana su ka hau babban titin Kanon zuwa Zariya a kusa da Tashar Yari a wani gari da a ke kira Dan Marke, don gudanar da ta’asar da su ka saba ta tare hanya tare da kashe rayukar matafiya da kwashe masu duniya.
Cikin ikon Allah sun datse hanyar cikin karamin lokaci ne sai rundunar ’yan sanda na shiyar makarfi suka sami labarin hakan wanda ya sa su ka dira wajen, don tarwatsa shirin ’yan fashin kuma cikin ikon Allah sun same su a wannan waje inda su ka yi karo da juna da ta kai da kashe biyu daga cikin ’yan fashin a nan take saura su ka ranta a na kare.
Tuni ’yan sandar su ka kwashi gawarwakin ’yan fashin zuwa babban ofishinsu da ke cikin garin Makarfi, don cigaba da bincike a kansu.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a kan barayi ya nuna cewa cikin gawarwakin guda biyu akwai bakon haure kuma an same su da layar zana ko ya daura a jikinsa.
SP Shuibu Patiko shi ne DPO na yankin Makarfi wata majiya ta tabbatar ma na cewa faruwar haka ya tara dukkan shugabannin Fulani, don su ganiwa idonsu abin da ke faruwa da ya ke dukkansu ’yan Fashin alamu sun nuna matasan Fulani ne.
Binciken ya tabbatar da cewa DPO ya ja hankalin shugabannin Fulanin da su kula da tarbiyar yaransu don kaucewa fadawarsu cikin muguwar sana’ar ta fashi da makami.
Haka kuma wakilinmu ya zanta da mutanen gari a kan samun nasarar da rundunar ’yan sandar su ka yi.
Wani bawan Allah da ya bukaci a sakaya sunansa bisa wasu dalilai ya ce, wajibi a yaba wa jami’an tsaron da su ka gudanar da wannan aiki wato DPO na Makarfi da yaransa don barayin sun buya wannan yanki, amma zuwansa an sami sauki, domin da kansa ya ke fita faturol wannan lokacimma da kanshi yaje inda barayin suka sa get din kuma dashi akayi artabun don haka jama’ar makarfi da yabo ta musamman ga DPO makarfi.
Bugu da kari jama’ar su bukaci gwamnati dasu kara masu kayan aiki don ci gaba da kare rayukar jama’ar da dukiyoyinsu.
Dubban jama’a ne sukayi dafifi don bai wa idansu abinci a yayin da a ka bajekolin gawarwakin a harabar ofishin ’yan sandan da ke a garin Makarfin.
DPO na shiyar ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce, ba zai ce komai ba bisa dokar da a ka ba su a kan hira da manema labarai.
Hoton na kasa gawarwakin yan fashinne da a ka kashe a hanyar kano zuwa Zariya a daidai garin Dan Marke karamar hukumar Makarfi jihar Kaduna.