Daga Umar Faruk,
Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi a jiya ta nemi hadin kai tsakaninta da wakilan kafafen jarida a jihar ta Kebbi.
Bukatar hakan ta fito ne daga bakin sabon Kwamishinan yan sanda CP Adeleke Adeyinka Bode da aka turo a jihar yayin wata zayara da ya kai a ofishin wakilan kafafen yada labaru da ke a jihar ta Kebbi a jiya a Birnin-Kebbi. Inda ya bayyana cewa” a matsayina na sabon Kwamishinan yan sanda da aka turo a jihar ta Kebbi naga yazama wajibi gare ni na kai ziyara ga masu ruwa da tsaki a duk fadin jihar ta Kebbi wanda Yan jaridu na daya daga cikin masu ruwa da tsaki a jihar domin suna ilmanta da jama’a abin da ke faruwa a cikin jihar da kuma kasa baki daya.
Saboda hakan ne nake neman hadin kan yan jaridu a duk fadin jihar ta Kebbi domin rundunar yan sanda tayi aiki kafada da kafada domin kadakar da al’ummar musamman ga irin rashin tsaro da ake fama dashi a wasu jahohin kasar nan da kuma bayyana wa al’ummar illolin aikata laifufuka a cikin yankunansu da kuma kananan hukumomi har zuwa matakin jihar da kasa bakin daya, inji CP Adeleke Adeyinka Bode yayin da yake jawabi ga wakilan kafafen yada labaru a ofishinsu da Birnin-Kebbi a jiya”.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar Kebbi da su cigaba da taimakawa rundunar yan sanda wurin bada bayanan sirri ga rundunar kan duk wani laifufuka da ake aikatawa lungu da sako na fadin jihar ta Kebbi.
Daga karshe Kwamishinan Adeleke Adeyinka Bode ya godewa wakilan kafafen yada labaru da ke Birnin-Kebbi kan bashi tabbacin hadin kai tsakaninsu da rundunar ta yan sanda a jihar kebbi.