Umar A Hunkuyi" />

Rundunar ‘Yan Sandan Abuja Ta Cafke Sarkin Ushafa Bisa Lafiin Kisa

Rundunar ‘Yan sanda ta babban birnin tarayya ta kama Sarkin Ushafa, da ke gundumar Bwari, Alhaji Mohammed Baba, a sakamkon zargin kashe wani dan sanda da jama’a suka yi a fadar na shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Anjuguri Manzah, ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, a Abuja.
Ya ce shi ma Sakataren fadar Sarkin, Mista Danlami Busa, an kama shi a bisa mutuwar dan sandan.
Manzah ya ce, an kashe ASP Eric Isaiah, ne a fadar Sarkin a lokacin da yake kokarin kama wani mai suna, Moses Peter wanda ake yi wa lakabi da Dogo, wanda kuma ake tuhumar sa da aikata kisan kai.
Ya ce wani mai suna Domnic Emmanuel, a ranar 21 ga watan nan na Jnairu ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda da ke Bwari, cewa dan’uwansa mai suna Moses da aka sanya shi aikin gini an same kuma a sume a bayan wani hari da aka kai masa har aka ji masa raunuka.
A cewar Manzah, dan’uwan na shi ya shaida wa ‘yan sanda cewa, an garzaya da Moses zuwa Asibiti domin yi masa magani, kuma ya bayar da bayanin ko su waye suka aikata masa wannan mugun aikin kafin mutuwar sa.
Ya ce Peter da ake yi wa lakabi da Dogo da kuma wani mai suna John su ya ambata da yake zargi da aikata masa aika-aikar.
A cewar sa, a kan hakan ne babban jami’in ‘yan sanda na ofishin yanki da ke Bwari ya aike da mutanan sa domin su je su bincika a kauyan na Ushafa.
Ya masu binciken da suka isa sun ga Peter din inda suka bi shi, amma sai ya ki yarda a kama shi, inda kuma ya gayyaci abokanan sa da suke a kusa da wata mashaya.
Manzah ya ce sai abokanan na shi suka dage da cewa sai dai a kai maganar a fadar Sarkin na Ushafa, kafin ‘yan sanda su kama shi din.
Ya sai ‘yan sandan biyu masu bincike suka yardan wa mutanan suka amince da a je fadar Sarkin na Ushafa, inda suka sadu da Sakataren Sarkin.
“A maimakon ya magance matsalar sais hi Sakataren Sarkin a bisa umurnin Sarkin ya zuga mutanan inda suka hau kan ‘yan sandan da duka.
“A dalilin hakan ne aka karo wasu ‘yan sandan domin su taimaka masu a karkashin marigayi ASP Eric Isaiah, da kuma wasu ‘yan sandan guda uku.
“Sun iso wajen a cikin motar ‘Yan sanda Hilud, wacce aka yi amfani da ita wajen ceton sauran ‘yan sandan biyu wadanda suka sami guduwa tare da wanda ake tuhumar Peter.
“Abin bakin ciki sai mutanan suka hau kan ASP Eric Isaiah, inda suka kasha shi, a bayan da suka jikkata sauran ‘yan sandan.
Manzah ya ce, Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, Mista Bala Ciroma, ya yi tir da kisan dan sandan da aka yi.
Ya ce Kwamishinan ‘yan sandan ne ya yi umurni da a kama wadanda suka kashe jami’in ‘yan sandan domin su fuskanci hukunci.

Exit mobile version