Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Rundunar ‘Yan Sanda jihar Kano ta bayyana kama Abubakar Isma’il mai shekara 30 da haihuwa wanda ake zargi da kashe jami’in dan sanda daya da kuma yin garkukwa da wani baturen kasar Jamus mai suna Kreser Michael, ma’aikacin kamfanin Dantata & Sawoe a Kano.
Idan za’a tuna a ranar 16 ga watan aprilun shekara ta 2018 wasu ‘yan bindiga suka sace injiniyan dan kasar Jamus bayan sun kashe dan sandan dake aiki tare dashi a wurin da suke aikin titin zuwa Karamar Hukumar Madobi a Kano.
Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyanawa manema labarai cewa an kama Isma’il ne a ranar 19 ga watan disambar shekara ta 2020 bayan watannin talatin da faruwar al’amarin.
Hakazalika wanda ake zargin ya amsa cewa sune suke kai hare hare a yakin Kananan Hukumomin Rimin Gado, Gwarzo, Karaye, Kiru, Bebeji da Tudun Wada duk a Jihar Kano da wasu makwabtan jihohi da suka hada da Kaduna da Katsina tsawon shekara biyar.
Haka kuma ya ambata sunayen wadanda ke cikin wannan tawaga tasu da suke aikata irin wannan ta’addaccin. ‘Yan sanda na kara zurfafa bincike domin damko sauran wadanda ake zargin” inji shi.
A wani cigaban rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta samu nasarar damke wani mutun mai suna Salmanu Muhammad dake unguwar Gwammaja wanda ake zargi da karya wani wurin ajiyar kaya dake unguwar Tal’udu a kwaryar birnin Kano.
Wanda ake zargin Salmanu Muhammad a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Kano Abdullahi Kiyawa yace an kama Salmannu ne a ranar 27 ga watan Nuwambar shekara ta 2020 tare da wata mota kirar Pick –up makare da kayan gini da kujeru na sata wanda aka kiyasata kudinsu ya tasamma Naira Miliyon takwas.
Dakarun ‘yan sanda ne suka damke motar da kuma Salmanu Muhammad Bashir mai shekata 36 dake unguwar Gwammaja a Jihar Kano. Kuma wanda ake zargin ya amsa laifin karya wurin ajiyar kayan dake unguwar Tal’udu a Kano.
Salmanu Muhammad ya bayyana yadda ya lalata makullin kofar sannan ya maye gurbinsa da wani sabo iri guda da wanda ya lalalta kuma ya kwashi kayan sama da Naira Miliyon takwas. An gano Mamallakin wurin ajiyar kuma ana ci gaba da gudanar da bincike. In ji Kiyawa