An bayyana rungumar Karatun Alkur’ani Mai girma da cewa shi ne hanya daya tilo ta samun saukin mummunan halin da ake ciki a kasarnan. Jawabin haka ya fito daga bakin Sheikh Dakta Nasidi Ababakar Goron Dutse alokacin da yake gabatar da jawabinsa a wurin bikin saukar Karatun dalibai 33 na Makarantar Rayadil-kur’an Gwani Muktar Mai Rigar Fata Littahafizul kur’an Goron Dutse.
Dakta Nasidi Ababakar yace rungumar Karatun Alkur’ani tare da kyautata karanta shi musamman ga kananan yara ‘yan Shekara 5,6 har Zuwa sama ne babbar hanyar fita daga halin da ake Ciki, yace ya zama wajibi a jinjinawa kokarin Malaman wannan makaranta musamman ganin wannan itace sauka ta biyu, amma kowa yaji karfin karatun wadannan yara, wanda hakan ke nuna irin jajircewar Malaman makarantar, don Haka sai ya bukaci iyaye da kuma wadanda Allah ya horewa da akara himmatuwa wajen hidimtawa Alkur’ani da ahlullahi. Shehin malamin ya jawo ayoyi da hadisan Annabi kan falalar karanta Alkur’ani da koyar da shi.
Shi ma shugaban Makarantar Gwani Sabo Mukhtar Mai Rigar Fata ya godewa Allah bisa samun irin wannan dama ta koyar da Alkur’ani da sauran fannonin ilimi, haka kuma ya bukaci karin hadin kan iyayen yara wajen ci gaba da ziyartar makarantar domin ganin matsayin karatun yaran nasu. Daganan sai ya bukaci wadanda suka Kammala saukar Alkur’anin da cewa yanzu ne ya kamata su dauka suka fara neman ilimi.
Shugaban Majalisar mahaddata Alkur’ani na kasa Gwani Aliyu Saluhu Turaki wanda kuma yana cikin wadanda suka biya allunan masu saukar ya bayyana farin cikinsa tare da yiwa Allah godiya, inda yace badon samun yara kanana dake karanta Alkur’ani da kuma haddace shi ba, ko shakka babu da yanzu ba haka labarin yake ba. Don haka sai bukaci iyaye da su kara himmatuwa wajen karfafawa yaran guiwa ta fuskar tallafa masu wajen gudanar da karatunsu.
Bikin saukar karatun ya samu halartar shehin Malami Dr. Nasidi Abubakar, Gwani Malam Lawan Sani Gaya, Sheikh Malam Isa Mamman Mai Rigar Fata, Gwani Aliyu Saluhu Turaki babban limamin Masallachin Juma’a Na Alhassan dantata, Gwani Bashir Salisu dan Ruwatsan, Gwani Mustapha Sheikh Mahmud Salga, Alhaji Sabo dan tata da sauran manyan mutane da Gwanayen Alkur’ani.