Rusa Ofishin Jakadanci: Ba Za Mu dauki Fansa Ba – Nijeriya

Fadar shugaban kasa ta ce ba za ta dauki wani matakin mayar da martini ba a kan kasar Ghana a kan rusa ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Accara ta kasar Ghana da aka yi a karshen makon da ya gabata.

Babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a kan harkokin manema labarai, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana wannan matsayin da gwamnatin ta tarayya ta dauka a fadar gwamnatin da ke Abuja, a ranar Laraba.

Ya ce, daukaR wannan matakin ya biyo bayan bayar da hakurin da Shugaban kasar ta Ghana, Nana Akufo-Addo, ne ya yi a kan faruwar lamarin.

“Shugaban kasar Ghana ya kira ya na mai nuna takaicinsa a kan abin da ya auku, sannan ya na mai bayar da hakuri ga Shugaban Nijeriya. Ina ganin ya nuna matsayin shugabanci a kan lamarin da kuma abin da Nijeriya za ta iya yi, wadanda su ne manyan kasashen Yammacin Afrika.

“Nijeriya ba za ta shiga fadan kan titi da kasar Ghana ba. Sam babu ta yadda hakan za ta faru. Don haka shugabannin kasashen biyu musamman shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ake matukar ganin kimarsa a nahiyar Afrika, har suna kiransa da Baba, don haka akwai bukatar ya nuna dattako da hakuri.

Mai Magana da yawun shugaban kasan y ace za a bi ta hanyar lalama da tattaunawa domin warware wannan matsalar.

“Matsalolin irin wadannan idan sun ta so, a kowane lokaci zai fi kyau ne a warware su ta hanyar lalama da tattaunawa a tsakani.

Sam ba wani fadan da za a yi a tsakanin Nijeriya da kasar ta Ghana, hakan ba zai taba faruwa ba,” in ji Garba Shehu.

Exit mobile version