Daga Ibrahim Muhammad,
Tun daga lokacin da Gwamnatin jihar Kano, qarqashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana aniyarta ta yiwuwar rushe gadar saman nan ta qofar Nasarawa, wacce ita ce gada ta farko a tarihin jihar da Tsohon Gwamnan jihar, Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya gina, mutane da dama ke ta nuna rashin jin daxinsu.
Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala na daga cikin waxanda ke ganin rashin dacewar hakan. A zantawarsa da jaridar LEADERSHIP A Yau ya bayyana ya bayyana iqirarin da tatsuniya kuma soki-burutsu da ba zai tava kankare irin soyayya da qauna da al’ummar jihar Kano suke yi wa jagoran Kwankwasiyyar ba.
Ya ce, idan hamayya ce ta sa Gwamnatin Kano ke neman rushe gadar, to ba su san irin wannan wace irin adawa ce ba, domin gadar an yi ta ne don amfanin al’ummar jihar Kano, kuma suna amfanarta, rusheta ba zai tava kawar da irin darajar da Kanawa ke baiwa Kwankwaso ba.\
Ya qara da cewa, ko a tasoshin talabijin in za a hasko qasar nan ko hotuna da ake bugawà na muhimman wurare, ana sanya wannan gada da Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya qirqire don al’ummar Kano, hakan ta sa an daxa xaga darajar jihar Kano ga kuma amfanar da ake yi wa gadar tana biyan buqatar fa’idar da ta sa aka yi ta na rage cinkoso bayan qawata gari da ta yi.
Ya ce, idan aka yi duba da Gadoji da Gwamnatin jihar Kano ta ke tutiyar ta yi, ba su da wata fa’ida ta sauqaqa wa al’umma.
Ya ce, Gadar sama ta ‘Yan Kura da ke kan titin Murtala Muhammad da Gwamnatin Kwankwaso ta gina da kusan kashi 70 kafin ya bar Gwamnati, kowa ya ga irin tsarinta da nagarta, amma Gadar qasa da wannan Gwamnatin mai ci ta yi na hanyar Madobi a yanzu ma tara ruwa ta ke yi kamar kududdufi, balle a lokacin damina, haka ma gadar qasa ta qofar ruwa sai tara cunkoso ta ke yi na ababen hawa kullum saboda rashin tsarinta.
Hon. Ali Namadi ya yi nuni da cewa abin da Allah ya so ko ‘yan hammayya sun so ko sunqi, soyayyarda al’umma suke yi wa Dokta Rabiu Musa Kwankwaso tana ci gaba ne da daxa xarsuwa a zukatan al’ummar Kano sakamakon irin ximbin abubuwan alhairi da ya gina musu, da ko da Gwamnati ta rushe gadar Nasarawa hakan ba zai rage karvuwa da amintar da al’ummar Kano suka yi wa Kwankwaso da komai ba, sai ma dai ya daxa qara masa kima.
Ya bayyana Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso da cewa jagora ne da ci gaban al’umma ne a gabansa, suna da masaniya na irin hidimar da ya yi wa Kano da kowa ya amfana, ya zama hantsi da ya leqa gidan kowa, ba tare da la’akari da siyasa ba, musamman yadda yake bunqasa ci gaban ilimi, ya xebi ‘ya’yan al’umma da ba su da hali ya tura su manyan jami’o’i na ciki sa a wajen qasar nan da suka je suka yi karatu a fannoni daban-daban na qwarewa da yawancinsu suka ci gajiya da suke hidimta wa kansu da ‘yan uwansu da kuma tallafa wa ci gaban al’umma.
Hon. Ali Namadi Dala ya ci gaba da cewa a lokacin da Xan takarar Gwamna Kano na jam’iyyarsu ta PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ke Kwamishinan ayyuka da gidaje na jahar Kano a Gwamnatin Kwankwaso aka gudanar da aikin gadar ta qofar Nasarawa, don haka ne ma saboda tabbatar da gaskiyar iqirarin da Gwamnatin Ganduje ta yi na cewa za ta rusa gadar saboda wai tana zaizayewa da nutsewa, ya rubuta takarda ya tuntuvi Kamfanin da suka yi aikin, sun kuma tabbatar wa da al’ummar jihar Kano cewa Gadar amincinta da ingacinta suna da yaqinin sai ta shafe shekaru 80 ba ta yi komai ba.
Daga nan Hon. Ali Namadi ya yi kira ga shugabanni da Allah ya baiwa mulki, kullum su sanya gaskiya da tsoron Allah da riqon amana a ayyukansu, su kuma duba su ga kafin su, wasu ne, kuma su ma wata rana ba su ba ne, za a riqa tunasu ne da irin ayyukan da suka yi na alkhari ko akasin hakan.