Idris Aliyu Daudawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home KIWON LAFIYA

Ruwa Da Amfaninsa A Jikin Dan Adam

by Idris Aliyu Daudawa
February 25, 2021
in KIWON LAFIYA
5 min read
Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Amfanin ruwa guda tara a jikin dan Adam idan ya sha da safe kafin ya fara cin abinci. Ruwa kamar dai yadda Bahaushe yake cewa abokin rayuwa ne gaba daya, wannan magana hakanan take, saboda kuwa, don amfanin ruwa mutum ba zai iya cewa ga yawansu ba. Shan ruwa da sassafe kafin cin komai yana da matukar amfani da babban muhimmanci. A duk ayyukan da mutum yake yi na yau da kullum, jikin sa yana bukatar karfi. Wannan dalilin ne yasa mutum yake shan ruwa domin ya yi maganin kishirwa.

Ga wasu amfanin shan ruwa da sassafe daga tashi bacci kafin a ci komai.
1. Shan ruwa da sassafe na samarwa da jikin dan Adam karin ruwa, musamman ma idan aka yi la’akari yawan awoyin da aka dauka aka yi ana bacci.
2. Shan ruwa kafin a ci abinci da safe na kara karsashi da karfin jiki.
3. Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tada kwakwalwa.
4. Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tsaftace jiki daga cututtuka
5. Shan ruwa da sassafe kafin a ci abinci na yakar cututtuka tare da kara garkuwa ga jikin dan Adam.
6. Shan ruwa da sassafe yana sa narkewar abinci kamar yadda ya dace.
7. Bugu da kari ma yana sa a rage kiba, ga masu irin kibar nan wadda ta wuce misali.
8. Yana gyara launin fata tare da sanya walwalin fata da walkiya.
9. Yana kariya daga ciwon koda tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta.

Yadda Shan Ruwa Yake Gyara Fatar Jiki:
Maganar da take bayyana cewar fatar jikin mutum zata yi kyau idan yana shan ruwa sosai wani abu ne da ya kasance kowa ya dace ya sani, amma abin mamakin shi ne babu wata sheda da za ta tabbatar da gaskiyar hakan. Claudia Hammond tayi bincike dangane da shi al’amarin.
Idan kana ganin fatarka tana kyau da sheki kamar matashi a koda yaushe, da alama a wani lokaci ka taba jin cewa shan ruwa da yawa yana fitar da guba da sauran abubuwan da jiki ba ya so kuma hakan zai sa fatarka ta yi kyau.
To sai dai wani abu shi ne yawan ruwan da ake cewa mutum ya sha ya bambanta daga wannan wuri zuwa wancan, domin a Amurka shawarar ita ce ka sha kofin ruwa takwas a kowacce rana, yayin da a wuraren da suke da zafi da yawa ake shawartar mutum sha fiye da haka saboda irin zufar da zai kasance yana yi.
To ko ma dai kofi nawa aka ce mutum yana sha, maganar dai daya ce, shan ruwa da yawa zai sa jikin mutum ya kasance da wadatar ruwa, wanda kuma hakan zai kasance wata laimar da za ta hana jikin shi bushewa.
Za ka yi mamaki ganin cewa wannan wani abu ne da ya zama ruwan dare gama duniya, amma babu wata sheda da za ta tabbatar da gaskiyarsa.
Mutum sai ya yi tsammanin an yi wani bincike ne mai yawa dangane da shi wannan al’amarin. a kan lamarin,sai dai kuma shi dan wanda aka yi ,an kasa mutane ne biyu.
Kashi na farko an sa su , su rika shan ruwa a kai a kai duk tsawon rana, sauran kashi na biyu kuwa, an sa su sha ruwansu kamar yadda suka saba a duk rana.
Bayan wata daya ko fiye da hakan sai kuma a duba bambancin kyawun fatarsu, aka tantance ko saboda yawan shan ruwa ne shi yasa yake gyara fata.
To maganar gaskiyaabin yana da wuya, a ce an yi irin wannan bincike, ta wani fannin watakila saboda ruwa abu ne da ba wata doka da za ta takaita ikon amfanin da shi ba, ga wani kamfani, wanda hakan zai sa babu wani kamfani da zai dauki nauyin irin wannan bincike, inda zai mayar da kudinsa har ma ya samu riba ta hanyar sayar da ruwa idan ya yi karanci.
Binciken da likitan fata Ronni Wolf wanda yake aiki a asibitin Kaplan Medical Centre da ke Isra’ila ya yi, ya gano wani al’amari daya ne kawai, da aka yi, wanda ya duba tasirin shan ruwa na tsawon lokaci a kan fata. Duk haka ma kuma sakamakon ya kasance mai rudani.
Sakamakon ya kasance ne, bayan sati hudu, rukunin mutanen da suka sha karin ruwa ( wanda ba a tace shi da sinadarai ba wato ruwan da ke fitowa daga dutse ko wata kafa ta Allah) fiye da yadda suka saba sha, ni’imar jikinsu ta ragu, abin da wasu ke ganin jikinsu ya rike ni’imar ne, yayin da wadanda suka sha ruwan famfo kuwa, aka ga karin ni’ima a jikinsu.
To amma duk da irin ruwan da kowanne kashin ruwa da mutanen ya sha, babu wani bambanci a jikin fatar tasu kan abin da ya shafi santsinta ko kyau.
Wanda hakan ke nuna cewa babu wani tasiri ko illa da rashin ruwa a jikin mutum zai yi wa fata.
Za mu iya tunawa ko yin nazari akan muhimmancin hakan, hakan ne ta hanyar tsaurin fatar. Hanyar itace yawan lokacin da fatar mutum za ta dauka ta koma yadda take daidai, idan aka tsunkuli mutum aka ja fatar sama.
Idan ba ka da ruwa a jikinka sosai fatarka za ta dan dade kafin ta dawo kamar yadda take.
To amma fa ba wai cewa idan shan ruwa kadan wani abu ne wanda bai da kyau ga fatar jiki ba, shan sa da yawa kuma ba za a iya cewa bai da amfani ba.
Hakanan abin zai kasance kamar a ce tun da rashin cin abinci zai jawo wa mutum cutar yunwa, cin abinci da yawa kuma a ce yana da kyau ba.
Har ila yau kuma kamar yadda Wolf ya nuna shi kuma, kamar ace ne tun da mota tana bukatar fetur, hakanan ma ana nufin yawan man fetur din da aka zubawa mata zai inganta yawan kyawun aikinta.
Wani abin da mutane suka yarda da shi kuma dai shi ne, cewa, idan ka sha ruwa da yawa jikinka zai adana shi.
Amma wai ya danganta da a lokacin da ka sha ruwan, misali, idan ka sha kofin ruwa da yawa a cikin mintina 15 za ka fitsarar da ruwan.
Idan kuma ka sha yawan wannan ruwan a cikin sa’oi biyu jikinka zai rike wannan ruwa.
Akwai binciken da ya nuna cewa shan ruwa mai yawan 500ml yana kara tafiyar jini a hanyoyin da ke cikin fata.
To amma ganin minti 30 bayan haka aka yi nazari, kan fatar, abin da ba mu sani ba, shi ne ko hakan ya kara hasken fatar.
Wata muhawarar kuma ita ce, kashi 30 cikin 100 na abin da fata take dauke da shi ruwa ne, wanda hakan yake sa, ta zama bulbul.
Wannan zai iya zama gaskiya, amma, sabuntar fata ya danganta ne da abubuwan da suka hada da kwayar halitta da zafin ranar da ke samunta da kuma illar shan taba.
To abin da ke daure kai a nan, shi ne, ina maganar cewa shan ruwa kofi takwas a rana yana da amfani, ta samo asali.
Babu ko wata tantama, ruwa shi ne sinadari mafi muhimmanci a jiki, wanda idan babu shi za mu mutu cikin ‘yan kwanaki, kuma ba shakka akwai karin amfanin da yake tare da isasshen ruwa a jikin mutum.
A wani bincike da aka yi a shekarar 2010 an gano shedar mai gamsarwa da take nuna cewa ruwa yana rage yawan tsakuwar cikin koda a jikin wadanda dama tuni suke da ita.
Amma kuma babu wata sheda kwakkwara ta wasu alfanun da aka danganta su da ruwa a jiki.
Ana ta jayayya a kan ka’idar shan kofin ruwa takwas a rana, inda ake ta ce- cuke game da yawan ruwan, da ake bukata da zai wanke guba daga cikin koda, da kuma ko ruwa yana taimakawa, ko ba ya taimakawa sha’awar cin abinci da mutum yake yi.
Komai dai ya danganta ne ga yadda yanayin zafi yake, da kuma yadda mutum yake aikata al’amuran shi.
Wata al’mara kuma ita ce, yadda ba a ma la’akari da muhimmancin sauran abubuwa na ruwa a jikin.
Ba wai sai abu ya kasance ruwan na zahiri ba, domin ai harma kayayyakin abinci suna dauke da yawan ruwan da mutum bai yi wani tsamman ba.
Yawan ruwan da muke samu a kayayyakin abinci ya dogara ne da inda muke zaune.
A kasar Amurka kashi 22 cikin 100 ne, amma kuma a Girka, inda mutane suka fi cin ‘ya’yan itace da ganyayyaki abin ya fi haka.

SendShareTweetShare
Previous Post

Farashin Dizel Ya Yi Tashin Gwauron Zabi

Next Post

Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

RelatedPosts

Cutar Korona

Abubuwa Takwas Da Aka Koya Shekara Daya Bayan Bullar Cutar Korona (1)

by Idris Aliyu Daudawa
1 day ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa, Koda kuwa bayan an yi ita...

Lassa

Yadda Zazzabin Lassa Ya Lakume Rayuka 176 A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
5 days ago
0

Daga Abubakar Abba, Hukumar dakile  yaduwar cututtuka ta kasa NCDC...

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

Uku Daga Cikin Cututtukan Kansa Da Suka Fi Hadari

by Idris Aliyu Daudawa
1 week ago
0

Daga Idris Aliyu Daudawa Masana harkokin lafiya sun yi tabbacin...

Next Post
Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

Na Fara Tunanin Ta Yadda Za Mu Doke PSG – Koeman

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version