Abdulazeez Kabir Muhammad" />

Ruwan Sama Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane A Garin Jibia, Katsina

A jiya ne a garin Jibia dake jihar Katsina ruwan sana yayi sanadiyar mutuwar mutune tare da rusa gidaje masu yawa.

Rahotanni da ba a tabbatar da shi ba, ya nuna cewa akalla mutune 25 suka mutu yayin da suka rasa mutane da dama. Har ila yau kimanin gidaje 80 da dabbobi musu yawa aka rasa a lamarin da ya faru.

An fara ruwan sama tare da iska mai karfi da misalin karfe 11 na daren jiya inda ruwan ya kai har zuwa karfe 3 na safe wannan safiya.

Unguwanni da abin yafi shafa sun hada da Unguwar Kwa-kwa, Unguwar Mai Kwari, Tudun Takari da Dan Tudu.

Mai garin Jibia, Rabe Rabi’u ya shaida wa manema labaru cewa, sama da 25 ne suka mutu. Ya kara da cewa an gano gawawwaki 19 da kuma binne su.

 

Exit mobile version