Sanusi Chen" />

Sabbin Alkaluma Sun Nuna Gaskiyar Yadda Tattalin Arzikin Kasar Sin Yake Ci Gaba

A yayin bikin kaddamar da cikakken zama karo na farko na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 13 da aka shirya a watan Maris na bara, a cikin “rahoton ayyukan gwamnati” da Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya bayar, ya dauki alkawura 36 kan yadda za a bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma da dai makamatansu a shekarar 2018. A yau Juma’a, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, an cika dukkan wadannan alkaruwa 36. A lokacin da ake fama da ringingimun tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasar Sin da Amurka a bara, tattalin arzikin kasar Sin kuma yake fuskantar matsin lamba sosai, ba abu ne mai sauki ba kasar Sin ta samu wannan kyakkyawan sakamakon da ake fata, sakamakon haka, ya mayar da martani sosai ga wasu kalaman da ake cewa wai tattalin arzikin kasar Sin zai durkushe.

Alkaluman da aka wallafa a shafin intanet na gwamnatin kasar Sin, sun nuna cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin wato GDP, da yawan hauhawar farashin kayayyakin masarufi, da yawan mazauna birane wadanda suka samu ayyukan yi, da yawan mutane da ba su da ayyukan yi da dai makamatansu, dukkansu sun cimma burin da aka kafa a bara, har ma a wasu fannoni, an cimma buri fiye da kima. Alal misali, yawan mutanen da suka samu ayyukan yi a birane ya kai miliyan 13.61 maimakon miliyan 11 bisa shirin da aka tsara. Sannan yawan mutanen da suka kubuta daga kangin talauci ya kai miliyan 13.86 maimakon miliyan 10 da aka shiri. Bugu da kari, yawan kudin da aka kashe kan wayar salula ya ragu da 63% maimakon 30% bisa shirin da aka tsara. Dadin dadawa, yawan kwal da aka haka a kasar Sin ya ragu da ton miliyan 270, maimakon ton miliyan 150 bisa shirin da aka tsara.

A shekarar 2018, an samu wani rahoto mai kyau dangane da ci gaban tattalin atzikin kasar Sin gami da na al’ummarta. Sai dai, har yanzu wasu sun nuna shakku kan gaskiyar alkaluma masu alaka da ci gaban tattalin arzikin Sin. Hakika idan aka yi nazari cikin tsanaki, za a fahimci cewa shakkun da wasu ke nunawa ba shi da tushe. Yanzu masana da masu kula da harkokin tattalin arziki na kasar Sin dukkansu sun yarda cewa, akwai ma’aunan tattalin arziki guda uku, wadanda ke da alaka da ma’aunin GDP, wato yawan kudin kayayyakin da ake samarwa a gida. Sa’an nan wadannan ma’aunai guda 3 su ne: yawan wutar lantarki da aka samar, da yawan kayayyakin da aka yi jigilarsu, gami da kudin shigar kasa a fannin biyan haraji. A kan yi amfani da ma’aunan 3 wajen tabbatar da cewa ko adadin GDP din na gaske ne. Sa’an nan a ranar Alhamis da ta gabata hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar da wani rahoto game da ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma na kasar Sin a shekarar 2018, inda aka nuna cewa, a cikin shekarar 2018, yawan wutar lantarki da kasar Sin ta samar ya karu da kashi 6.8% bisa na bara, kana yawan kayayyakin da aka yi jigilar su ya karu da kashi 7.1%, yayin da kudin da gwamnatin kasar ta samu ya kai Yuan biliyan 18,000, jimilar da ta karu da kashi 6.2%. To, a nan za a gano cewa, karuwar da aka samu bisa wadannan ma’aunai guda 3 sun zama ginshikin karuwar GDP din kasar da kashi 6.6% a shekarar da ta gabata.

Idan har wadannan alkaluman suna da sarkakiya, zai kuma yi wuya a iya fahimtar ma’anarsu, to, yanayin zaman rayuwar jama’ar kasar Sin zai nuna ainihin yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki a bara. A kwanan baya, yayin hutun mako guda na bikin gargajiyar kasar Sin ta Chunjie, wato “Bikin Bazara” a Hausance, an kafa wasu matsayin bajinta a fannin sayayya a kasar Sin, inda darajar kayayyaki da abinci da wasu kamfanoni suka sayar ta zarce Yuan biliyan 1000, adadin da ya karu da kashi 8.5% bisa makamancin lokacin bara. Sa’an nan yawan masu yawon shakatawa da suka ziyaci wurare daban daban na kasar cikin wannan mako na musamman ya kai miliyan 415, jamilar da ta karu da kashi 7.6%. Har wa yau a fannin yawon shakatawa, an samu kudin da ya kai Yuan biliyan 513.9, adadin da ya karu da kashi 8.2% bisa makamancin lokacin bara. Ban da wannan kuma, a karo na farko yawan cinikayyar da aka yi ta tsarin biyan kudi ta yanar gizo ta manhajar China Union Pay ta zarta triliyoyi, wato ya karu da kashi 71.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. A duk tsawon shekarar, jama’ar kasar sun nuna karfin sayen kayayyaki sosai, yawan tallafin da wannan bangare ya bayar kan karuwar GDP ta hanyar sayen kayayyaki ya kai kashi 76.2 cikin dari, wato ya karu da kashi 18.6 cikin dari bisa na bara. A matsayinsa na daya daga cikin muhimman gishinkan inganta tattalin arziki, bangaren sayen kayayyaki na kara taka muhimmiyar rawa, har ma ana iya gano alamar karuwar matsayin sayen kayayyaki.
“Dole sai an tashi kafin a iya cimma kowane irin buri”. A shekarar 2018, an fuskanci tabarbarewar tattalin arzikin duniya, kuma an yi ta samun kiki-kakar cinikaya, musamman ma rikicin cinikayya da kasar Amurka ta tayar ya sanya an damu da abin da ka iya samun tattalin arzikin duniya. Bisa wannan yanayin da ake ciki, saurin karuwar GDP na kasar Sin ya kai kashi 6.6 cikin dari, hakan ya sa an cimma burin kimanin kashi 6.5 cikin dari da ake fatan samu a cikin rahoton ayyukan gwmanati na shekarar 2018.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddadawa, cewa “fatan jama’a kan rayuwa mai kyau,shi ne burin da za mu yi kokarin cimmawa”. An kafa burin ci gaba ne da nufin kyautata zaman rayuwar jama’a. A shekarar 2019, za a gamu da jerin wahalhalu da matsaloli yayin da muke kokarin neman ci gaba, amma nasarorin da kasar Sin ta samu a shekarar 2018 sun kara kwarin gwiwa ga al’ummar duniya, ana iya cewa, jama’ar kasar Sin za su more sakamako mai kyau tare da duniya baki daya.

(Sanusi, Bello, Bilkisu, Ma’aikatan CRI Hausa)

Exit mobile version