Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ta rantsar da sabbin dalibai dubu bakwai da dari daya da hamsin da shida (7,156) da suka samu guraben karatu a zangon karatun 2019/2020 da na shekarar 2020/2021.
Da ya ke jawabi a wajen bikin wanda ya gudana a reshen jami’ar da ke Yelwa, Mukaddashin shugaban jami’ar ATBU, Farfesa Muhammad Ahmad Abdul’azeez, ya shaida cewar an samu hadewa tare da bada izinin karatun rukuni biyu a lokaci daya ne sakamakon tarnakin da annobar Korona ta jawo wanda hakan ya tilasta ba a baiwa daliban 2019/2020 izinin shiga jami’ar ba sai yanzu.
Mukaddashin jami’ar Farfesa Abdul’azeez ya jawo hankali tare da gargadin sabbin daliban da su tsame kawukansu daga fadawa cikin sha’anin shaye-shayen miyagun kwayoyi, satar jarabawa, shiga kungiyoyin asiri da sauran munanan dabi’u, yana mai cewa dukkanin dalibi ko dalibar da suka karya wani dokar jami’ar, akwai ladabtarwa daki-daki da dokokin makaranar ya tanadar.
Ya ce, “Saboda iyaka wuraren da muke da su, ba za mu iya baiwa dukkanin wadanda suka nemi izinin karatu a wannan jami’ar dama ba, don haka duka-duka, mun takaita adadin dalibai 7,158 da muka baiwa damar yin karatu a wannan lokacin.”
Ya ce, a halin da suke ciki, dole ne a yi nazarin kalubalen da ke akwai na annobar Korona da take dagula lamura tare da bin matakan da suka dace wajen kariya daga kamu da cutar, don haka ne ya ce a matakinsu na jami’a, sun dauki matakin babu mai shiga cikin aji ko harabar jami’ar ba tare da kyallen rufe hanci da baki ba, kana sauran matakan kariya daga cutar duk suna bi.
Ya ce sun tabbatar daliban jami’ar na tafiya daidai da dokokin da gwamnati ta samar na kariya daga cutar da suka hada da yawan wanke hannu, rage cinkoso hatta aji, sanya abin rufe hanci da baki da sauran matakan da suka tabbatar daliban na bi, ya kuma yaba da yadda ake bin matakan da suka dace na kariya daga cutar.