Sabbin Ministocin Buhari: Tawagar Ma’aikata A Ka Zabo – Kwamitin PSC

PRESIDENT BUHARI ATTENDS DAY-2 OF PRESIDENTIAL MINISTERS RETREAT 14. L-R; Sulieman Adamu, Dr Muhammed Mohmood and Zainab Ahmed, Alhaji Muhammed Sabo Nanono and one other during the Day-2 of the Presidential Retreat for Ministers designate held at the State House Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE. AUG 20 2019.

Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC) ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu kan sabbin ministocin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zabo, wazanda za a rantsar a yau.

Kwamitin ya ce, ministocin tawagar ma’aikata masu himma ne, wadanda za su yi aiki tukuru yadda ya dace ba tare da watsawa mutane kasa a ido ba.

Wannan bayanin na kwamitin PSC yana kumshe ne a wata takardar da Daraktan sadarwa da tsare-tsaren PSC, Mallam Gidado ya fitar kuma ya rattabawa hannu. Takardar ta shaida cewa, irin zakakuren da shugaban kasa buhari ya zabo ‘yar manuniya ce kan irin muradin da yake da shi na son tsamo jama’a daga talauci.

Mallam Gidado Ibarahim ya ce, ministocin na Buhari da kuma ma’aikatun da za a basu zai watsawa ‘yan adawa kasa a ido, musamman ma wadanda ba su ganin duk wani alheri ko ci gaba tattare da gwamnatin.

Haka kuma Kwamitin PSC ya bukaci ‘yan Nijeriya da su bi a sannu da ‘yan siyasan da suke fakewa a rigar kabilanci da bangaranci wurin haifar da rarraba a tsakanin ‘yan kasa, duk domin cimma muradin kashin kansu.

Mallam Gidado ya ce; “Yana da kyau na yi gwari-gwari ga wasu masu kiran kansu ‘yan adawa da su daina kokarin yin kalaman batanci marasa tushe ta hanyar bata sunan Nijeriya da sunan adawa da Shugaban Kasa Buhari. Wannan sam ba daidai ba ne, ya sabawa hankali ma.

“Shugaban Kasa Buhari ya cancanci yabo kan irin kokarin da ya yi wurin cika alkawurran da yayi a lokacin yakin neman zabe, musamman a kan tsaro, yaki da cin hanci da rashawa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa. Yanzu kuma ya dora ne akan kokarin tseratar da ‘yan kasa daga kangin talauci.” Inji shi

Mallam Gidado ya yi nuni da cewa, kwanaki biyu da aka shafe ana  yin bita ga sabbin ministoci wanda fadar shugaban kasa ta shirya, wani abu ne dake kumshe cikin ajandar Buhari ta son ciyar da Nijeriya gaba.

Exit mobile version