SABC: Alakar Moriyar Juna Dake Tsakanin Sin Da Afirka Ta Samu Yabo
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

SABC: Alakar Moriyar Juna Dake Tsakanin Sin Da Afirka Ta Samu Yabo

byCMG Hausa
3 years ago
SABC

Wani rahoto da sashen labarai na hukumar yada labarai ta kasar Afirka ta kudu (SABC) ta fitar, ya yaba da irin nasarorin da aka cimma, karkashin hadin gwiwar kasashen Sin da Afirka, inda ya bayar da misali da hadin gwiwar cinikayya tsakanin sassan biyu, da batun kawar da fatara, da kuma karfafa tattalin arziki a nahiyar Afirka.

Wani sharhi da aka wallafa a shafin watsa labaran hukumar ta SABC, a watan Yulin wannan shekara, ya bayyana cewa, duk da kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, cinikayya tsakanin Sin da Afirka, ta yi nasarar kaiwa matsayin da ba a taba gani ba a shekarar 2021, kuma kasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta, na kasa mafi yawan masu zuba jari a Afirka cikin shekaru 10 da suka gabata.

  • Darajar Cinikayyar Sin Da Ketare Ta Karu Da Kaso 9.4

A cewar sharhin, wannan na zuwa ne, a lokacin da nahiyar ke matukar bukatar zuba jari kai tsaye da samar da guraben ayyukan yi.

Alkaluman kididdigar da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, darajar cinikiyya tsakanin kasashen Sin da Afirka a shekarar 2021, ta kai dalar Amurka biliyan 254.3, karuwar kashi 35.3 bisa 100 kan na shekarar da ta gabata, daga ciki, Afirka ta fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 105.9 zuwa kasar Sin, wanda ya karu da kashi 43.7 bisa dari kan na shekarar da ta gabata.

Sharhin ya ci gaba da cewa, hadin gwiwar Sin da Afirka na ba da gudummawa, wajen samar da ayyukan yi a nahiyar, inda ake samar da guraben ayyukan yi ga mutane 18,562 a Afirka a kowace shekara.

Wannan ya taimaka wajen rage matsalar rashin aikin yi, da inganta kokarin da ake yi na kawar da talauci da yayata bukatar zuba jari. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Karya Ne, Ban Fice Daga APC Ba – Osinbajo

Karya Ne, Ban Fice Daga APC Ba - Osinbajo

LABARAI MASU NASABA

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version