Connect with us

MANYAN LABARAI

Sabo Da Wayar Hannu Ya Zame Wa Al’ummar Jihar Kogi Alakakai

Published

on

Jama’ar jihar Kogi sun fara kukawa game da yadda mugun sabo da wayoyin hannu musamman ga matasa da mata, ke neman zame wa al’ummar jihar alakakai, sun yi korafin ne a daidai lokacin da aka gudanar da wani binciken jin ra’ayin jama’a.

Ana ganin yawan matasa ‘yan tsakanin shekaru 16 zuwa 25 da suka yi mugun sabo da wayoyin hannun su ya kai kashi 75 cikin 100, suna amfani da manyanwayoyin hannu matuka wajen jin waka da shiga intanet da kuma kiran waya.

Baya ga wannan suna amfani da su sosai wajen shiga shafukkan sada zumunta irinsu Facebook, WhatsApp, Instagram da sauransu, sannan suna amfani da wayoyin wajen yin hoto, musamman hoton yayi na dauki da kanka (selfie) da sauran abubuwan masu kama da haka.

Sannan an kuka da yadda matasa suke amfani da wayoyinsu na hannu wajen kalle-kalle na fina-finan batsa, har wasu na ganin lallai bai kamata iyaye su sake ma yayansu kanana wayoyin hannu ba, saboda hakan zai yi tasiri matuka wajen bata tarbiyyarsu.

Wata babbar matsala da manyan wayoyin hannu ke haifar wa ta hada da kawo matsala tsakanin ma’aurata, musamman masu karancin shekaru, mugun sabo da suke yi da wayoyinsu na hannu yana matukar haifar da matsala a zamantakewar aurensu, wanda har yana kai wa da rabuwar auren.

Duk wayoyin suna da matukar amfani, amma yadda mutane suke mugun damfaruwa da wayoyinsu har ta kai ga sun hana su yin wasu abubuwa masu amfani shine babbar illar da ake fuskanta yanzu.
Advertisement

labarai