Saboda Annashawa Na Kashe Budurwata, Ba Don Tsafi Ba

Daga Abubakar Abba

Wani Dalibi mai shekaru ashirin da biyu mai suna Oweniwe Chukwudi da ke zango na biyu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Rufus Giwa Owo, a Jihar Ondo da ake zargin ya kashe budurwar sa har lahira don yin asri, ya musunta zargin da ake masa. Sai dai, Oweniwe ya ce ya hallaka tane don kawai jin dadi.

Acewar Oweniwe,” Ban cire mata komai daga sassan jikinta ba, na kawai kashe ta ne don jin dadi, bayan na yi lalata da ita a cikin daji, kafin na hallaka ta.”

Ya ce, “ ba abin da ya hada ni da wata kungiyar asiri, bayan na hallaka ta ne, sanan nayi tunanin cewar, nayi babban kuskure sai kuma na fara kuka ba kakkautawa.”

Oweniwe ya bayyana hakan ne bayan da jami’an ‘yan Sanda na farin kaya da ke jihar suka cafko shi.

Matashin wanda iyayensa manoman Rogo ne a yankin  Ogbese da ke Jihar, ya ci gaba da cewa, sherin shedan ne yasa ya aikata kisan.

Oweniwe da marigayiyar Adeyeye Nifemi duk su na zango na biyu na karatu a sashen bangaren gwaje-gwaje-gwaje da  kimiyya.

An ruwaito cewar Oweniwe, ya yi tattaki har na tsawon kilo mita goma zuwa sha biyar zuwa kauyen Ayede Ogbese daga makarantar don ya aikata ta’asar.

Bayan da ya biya  bukar sa da Marigayiyar, ya barta a yashe a dajin a bisa tunanin sa ta riga ta mutu, inda sai da bayan ya dawo gida ne washe gari, ya same ta da ranta.

Bayanai sun ce, Oweniwe ya koma zuwa dajin inda ya bar dalibar tare da wani da ya raka shi don yin asirin, sai ya cika da mamaki da ya ganta bata mutu ba.

Oweniwe ya fake da nufin taimaka wa burwar tashi, ta hanyar daukar ta zuwa wani wuri kusa da wani gidan Mai da ke Ilu Abo, inda ya sake murde ta. Har ila yau ba ta dai mutum ba, sai ya samu Dutse ya yi ta maka mata har sai da ta cika.

Kwamishinan Rundunar  ‘yan Sanda, Hilda Harrison ya ce, bayan an bi sahu ne aka cafko wanda ake zargin kuma ya amsa  laifinsa lokacin da ake bincike.

Harrison ya ce, za a gurfanar da Oweniwe a gaban kotu in Rundunar ta kammala binciken ta.

Exit mobile version