Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa, ta yanka filotai a Gidan Rediyon Manoma na Jihar Kano da ke Unguwar Tukuntawa ne sakamakon barazanar tsaro da gidan rediyon ke yi ga al’ummar da ke kewayansa.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka, yayin tattaunawarsa da manema labarai a Kano.
Muhammad Garaba ya ce, tun a shekarar 2010 aka daina amfani da wannan gidan rediyo, sakamakon bude makamancinsa da aka yi a garin Jogana. Ya kara da cewa, gwamnati ta so ta yi gidan rediyon manoma a wannan wuri, amma sakamakon tsofaffin kayan aiki da gurin ke da shi sai aka mayar da shirin manoman zuwa gidan rediyon Kano na Bello Dandago.
Ya ce, ko a ‘yan kwanakin da suka gabata, sun samu rahotannin da ke cewa an samu gawarwaki har guda uku a cikin Gidan Rediyon. Hakan yasa Gwamnati ta duba tare da ganin cewa bai kamata a bar filin a haka ya zama matattarar ‘yan iska ba.
“Duk wanda yake wannan wuri ya san fili ne na gwamnati, sannan a lokacin Marigayi Kabo Idris Shugaban Gidan Rediyon Kano, ya ba da umarnin masu noma da ajiye ababen hawa su dena, amma aka kyale su. “Yanzu lokaci ya zo, saboda barazanar tsaro da mugan abubuwan da ake yi a gurin yasa gwamnati ta yanka gurin,” a cewar tasa.
Ya kara da cewa, ba dole ne sai gwamnati ta tuntubi wasu ba, idan har za ta saida wani guri da yake mallakinta. Ya ce, gwamnati za ta sanar da mutane ne kawai idan har gurin da take so ba mallakinta ba ne.