Connect with us

LABARAI

Saboda Kishin Jihar Kaduna Mu Ka Sayi Wa Gwamna el-Rufa’i Takardar Takara -Alhaji Abbas

Published

on

Yanzu haka wata kungiyar da suka kira kansu ma su kishin jihar Kaduna, da suka fito daga kananan hukumomin jihar 23, sun sayi wa  gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’I takardar takarar gwamna na zaben  shekara ta 2019.

Jagoran kungiyar, wani mai tallafa wa al’umma mai suna Alhaji Abbas Gambo Likoro, ya bayyana wa wakilinmu haka, jim kadan bayan sun mika wa  gwamnan jihar Kaduna, wannan takardar takara a gidan gwamnati da ke garin Kaduna.

Alhaji Abbas Lokoro ya ci gaba da cewar, duk wanda ya lura da yadda gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’I ke jan ragamar gwamnatin jihar Kaduna da kuma ayyukan da ya sa a gabansa, ya san gwamnan na bukatar ya ci gaba jagorancin jihar Kaduna bayan zaben shekara ta 2019.

Da kuma mai tallafa wa al’ummar ke tsokaci kan yadda gwamna Malam El-Rufa’I ke aiwatar da ayyuka a sassan jihar Kaduna, ya ce, gwamna ya san shugaba ne nagari da ya ke da  kyakkyawar kudurin ciyar da jihar Kaduna gaba a bangarori daban- daban na ci gaban al’ummar jihar Kaduna.

Da kuma Alhaji Abbas Likoro ya juya ga al’ummar jihar Kaduna , sai ya yi kira ga duk wani mai kishin jihar Kaduna da ya sanya kishin jihar a zuciyarsa ko kuma zuciyarsu, a lokacin zaben shekara ta 2019, ta yadda za a tabbatar da gwamna Malam Nasir El-Rufa’I a matsayin zababben gwamna karo na biyu, a shekara ta 2019.

A karshen ganawarsa da wakilinmu, Alhaji Abbas Gambo Likoro, ya  yaba wa al’ummar jihar Kaduna , musamman magoya bayan jam’iyyar A P C da suke jihar Kaduna,na yadda duk da matsalolin da gwamna ke fuskanta daga makiya jihar Kaduna,na yadda suke ba shi goyon bayan da suka dace, da ya sami damar aiwatar da ayyukan da al’ummar jihar Kaduna ke murna da su, da suka shafi bangarorin kiwon lafiya da ilimi da batun warware matsalolin ruwa day a gada daga gwamnatocin da suka gabata da bunkasa tattalin arzikin jihar Kaduna da kuma al’ummar jihar baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: