Abba Ibrahim Wada" />

Saboda Ronaldo Juventus Za Su Iya Cin Kofin Zakarun Turai

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Leonel Messi ya bayyana cewa komawar dan wasa Cristiano Ronaldo kungiyar Juventus yasa yanzu kungiyar tazama kungiyar da zata iya lashe kofin zakarun turai na wannan kakar.
Messi da Ronaldo dai sun shafe shekaru goma suna sharafinsu a duniya bayan da suka lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya sau biyar biyar kowanne acikinsu sai dai adawar ‘yan wasa biyun ta kare bayan da Ronaldo yakoma Juventus.
Messi ya ce, ya yi mamakin komawar Ronaldo Juventus saboda labarin yazo masa sabon abu amma kuma yace a kwallon kafa komai yana iya faruwa kuma yanzu yasa kungiyar Real Madrid bata da karfi sosai.
“Kowa ya san Real Madrid babbar kungiya ce mai cike da manyan ‘yan wasa da kuma tarihin lashe kofuna a duniya amma kuma tafiyar Ronaldo yasa karfinsu ya ragu sosai saboda rashinsa babbar matsala ce” in ji Messi
Messi ya cigaba da cewa “Juventus suna daya daga cikin manyan kungiyoyi a duniya sannan kuma zuwan Ronaldo yasa yanzu zasu kara karfi kuma zasu zama kungiyar da za’a dinga jin tsoro a duniya”
Tun bayan komawar Ronaldo Juventus ya zura kwallo 18 a raga a gasar Siriya A cikin wasannin daya buga yayinda kawo yanzu Messi yana da kwallaye 41 cikin wasannin daya bugawa Barcelona tsakain kofin zakarun turai da Laliga da kuma Copa Del Rey.

Exit mobile version