Saboda Arzikin Zinaren Arewa Ake Kashe Mana Mutanenmu – Shugaban Matasan Arewa A Kudu

Daga Yusuf Shuaibu

 

Gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda wanda zai ba ta damar yin amfani da jiragen yakin da ta siyo daga kasar Amurka. Wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka na zuwa ne bayan shefe tsawan lokaci da ake ta kiraye-kirayen gwamnatin ta yi hakan.

Musu sharhi kan harkokin tsoro sun bayyana cewa jiragen yakin da Nijeriya ta siyo daga Kasar Amurka za su taimaka wajen tunkaran ‘yan bindigar daji wadanda suka addabi Arewacin Nijeriya.

Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa a Kudancin Nijeriya, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci wanda ya saba sharhi game da tabarbarewar tsaro a Arewacin Nijeriya, ya bayyana cewa suna jin jita-jita na jawabin cawa Nijeriya ta siyo jiragen sama wanda za ta yaki ‘yan ta’adda, amma an ce ba a ba ta damar ta yi amfani da su ba sai dai a kan ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa a yanzu da gwamnati ta ayyana wadannan ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda tana da dama da za ta yi amfani da jiragen. Ya ce idan gwamnati da gaske take sai da shirya kawar da wadannan mutane, sai dai idan ba da gaske take yi ba, domin wadannan abubuwan sun yi yawa kuma mun sha fada wanda har gwamnati ta san da hakan.

A cewarsa, babu wadanda suke koma-baya sai ‘yan Arewa sakamakon irin wannan ta’addanci da ake yi wa ‘yan Arewa. Ya ce hanyar Kano zuwa Kaduna da kuma hanyar Kaduna zuwa Abuja ya zama ka ta fi da linkafaninka shi ne mafi a’ala idan zai maka amfani kenan.

Ya ce abubuwan sun yi yawa matuka gaya wanda a kullum gwamnati tana wayar a kan cewa ta yi kaza da kaza wanda ba a gani a kasa. Ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta dauki mataki wanda sun dade suna bai wa shawarwari, domin duk wasu jami’an tsaro suna karkashin gwamnati. Ya ce ya kamata gwamnati ta tsaya tace jami’an tsaro na kwai, saboda a cikin su akwai munafukai.

Har ila yau, ya bayyana cewa shugaban kasa ne mai hakkin tace jami’an tsaro na sirri wadanda za su dunga ba shi shawara, ba wai a kai masa labari ba ko ya gani. Ya ce ya kamata shugaban kasa ya samu wadanda ya yarda da su da za su dunga ba shi shawara kan yadda kasa ke ciki da abubuwan da take fuskanta na wannan lamari.

Da ya juya kan matsalolin ‘yan awaren IPOB na neman a raba kasar kuwa, ya bayyana cewa lamarin da ‘yan kungiyar IPOB suke kunno wuta kamar na kashe-kashen da suke yi wa jami’an tsaro da fararen hula wanda babu abin da ba sa yi kuma gwamnati ta sani.

Ya ce, “Mun sha fada wa gwamnatin Nijeriya ta kira shagabannin IPOB ta zauna da su tare da musu sharadi wajen ja musu layin abubuwan za su ja wa mutanensu kunne a kai, domin abubuwan sun yi yawa kuma gwamnbati tana sane tun ba za a ce ba ta sani ba, saboda sojoji nawa aka kai suka kashi, haka ma ‘yan sanda nawa aka kashe tare da fararen hula. Maganan da suke cewa a daina kai musu abinci, ai laifin ‘yan Arewa ne da ba su da kishi. Domin duk wani arziki da ake nema Allah ya bai wa yankin Arewa.

“Muna da gwal da sauran ma’adanai wanda kashen waje ke zuwa suna diba kuma su ne musabbabin kisan da ake mana a Arewa saboda a karkatar da hankulan mutane ta yadda za a dunga kashe al’umma ana samun damar diba,” in ji Alhaji Ya’u Galadanci.

 

Exit mobile version