Connect with us

RAHOTANNI

Sabon Dandarman Jubawa Ya Yi Godiya Ga Al’umma Kan Nadin Sarautarsa

Published

on

Sabon Dandarman Jubawa da ke karamar hukumar Garun Malam Alhaji Nuhu Alhassan ya gode wa daukacin mutanen da suka nuna masa goyon baya wajen samun wannan sarauta tare da yin kira gare su su kara taya shi da addu’a domin samun nasarar abin da aka dora masa.

Yana jawabine ga ‘yan jaridu a Legas, inda ya nuna farin cikinsa da wannan matsayi na Dandarman Jubawa da aka bashi a karamar hukumar ta Garun Malam.

Ya bayyana godiyarsa godiya ga Dagacin Jubawa, Alhaji Umaru Inuwa da mai girma Hakimin Garun Malam Alhaji Lawan Abubakar Madaki Ajiyar Rano.

Alhaji Nuhu Alhassan har ila yau shi ne sarkin hausawan Ikoto wanda ya gaji wannan sarauta daga mahaifarsa ta Dandarman da ke arewacin Nijeria cikin jihar Kano karkashin masarautar Rano.

Alhaji Nuhu ya nuna farin ciki mai yawa sarkin sasa sardaunan jihar yamma Alhaji Haruna Mai Yasin soboda kokarin da yake yi a nan jahar yamma na ganin an zauna lafiya da kuma wayar da kan jama’a a kan wannan cuta ta Korona.

Da cikin ‘yan majalissarsa akwai limamin fada Malam Sadik Abubakar Kabiyesi, Alhaji Hassan Ibrahim P.A. sarki, Alhaji Hassan Jega sardauna, sakatare Injiniya Haruna Musa, shugaban zabarmawa Alhaji Usman Kekere da Alhaji Hamza Garkuwa da waziri Alhaji Idris Hamisu, Alhaji idris makama.

Dandarman din ya jinjina wa ‘yan majalisarsa bisa wannan nasara inda ya ce ba tasa ba ce shi kadai har da su baki daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: