Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar

bySulaiman and CGTN Hausa
7 months ago
Sin

Kawance a tsakanin jihohin arewacin Najeriya da kamfanonin kasar Sin ba sabon abu ba ne, zan iya cewa an kwashi shekaru da dama ana yi, sai dai abin da ya ja hankalina a kwanan shi ne ziyarar da jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai ya kai jihar Kano da kuma kawancen da aka kulla a tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da wasu kamfanonin kasar Sin domin gudanar da wasu ayyukan raya kasa.

Ziyarar jakadan na Sin a fadar gwamnatin Kano ta kunshi kyakkyawan albishir ga jihar a kan karfafa alaka a tsakaninsu domin bunkasa ayyukan more rayuwa da bunkasa ci gaban masana’antu a jihar. Kana da yabawa da yadda Sinawa ke jin dadin gudanar da kasuwancinsu a jihar ta Kano ba tare da tsangwama ba.

  • Sin Na Fatan Dukkan Bangarori Za Su Guji Daukar Mataki Da Zai Ta’azzara Rikici A Gaza
  • Dakatar Da Gwamna Fubara: Tinubu Ya Naɗa Tsohon Hafsan Sojin Ruwa A Matsayin Mai Kula Da Jihar Ribas

Har ila yau, kasar Sin ta sha alwashin kulla kawance da jihar a fannonin noma na zamani da karfafa samar da wadatar abinci da kayayyakin more rayuwa da kuma bunkasa ci gaban ilimi, inda Jakada Yu Dunbai ya bukaci gwamnatin jihar ta yi kokarin cin gajiyar makudan kudin da kasar ke zuba jarinsu a Najeriya.

A can jihar Zamfara ma, gwamnatin jihar ta karbi bakuncin wasu kamfanoni na kasar Sin a fadarta da ke Gusau, babban birnin jihar inda aka tabbatar da hada hannu a tsakaninsu a fannonin samar da ingantattun fasahohin zamani da habaka noma, da sufuri da albarkatun ma’adanai da Allah ya huwace wa jihar.

Kamfanonin da suka je ziyarar bayan gwamna Dauda Lawal na jihar ya fara kai musu ziyara a kasar Sin a watan Fabrairun da ya gabata, sun hada da: Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co. Ltd, da kuma Tibet Ming.

A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar.

Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga.

Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar ana so a magance matsalar tsaron da ta hana arewacin Najeriya sakat dole sai an hada da magance zaman kashe wando, da bunkasa tattalin arziki da kuma samar da na-gartaccen ilimi.

Sabon yunkurin jihohin arewa na kulla kawance da kamfanonin Sin babu shakka zai bude kofofin karfafa tattalin arzikin yankin wanda Allah ya albarkace shi da kasar noma mai kyau fiye da sauran sassan Najeriya, sannan ga tarin albarkar yawan jama’a, da albarkatun sarrafa sabbin makamashi, domin kamfanonin Sin suna da kwarewar aiki da dimbin ayyuka na fasahar zamani ta yadda suke iya sarrafa albarkatu kalilan a samar da amfani mai yawa. Sannan suna da karfin zuba jari fiye da yadda ake zato, domin ko a watan Satumban 2024, gwamnatin jihar Neja da ke arewacin Najeriya ta rattaba hannu da wasu kamfanonin Sin guda biyu –COVEC da CREC a kan kwangilar dala miliyan 684 domin gudanar da ayyukan gona na musamman a jihar.

Tabbas, jihohin sun dauki hanya mai kyau da za ta fa’idantar, fatana shi ne a wayi gari yankin arewa ya dawo da martabarsa ta ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma.(Abdulrazaq Yahuza)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Bisa Daidaito Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Amfanar Da Kamfanonin Duniya

Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Bisa Daidaito Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Amfanar Da Kamfanonin Duniya

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version