Daga Hussaini Yero Zamfara,
Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Alhaji Abutu Yaro, ya dau alkawarin kawo karshen ‘yan bindiga da masu satar mutane wadanda suka gurgunta ci gaban tattalin arzikin jihar.
Kwamishina Abutu Yero, ya bayyana haka ne a loakcin da yake zantawa da manema labarai a Hedikwatar ‘yan sandan da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Kwamishinann ya kara da cewa,’Game da kalubalen tsaro a jihar wadanda suka hada da satar shanu da ‘yan fashi da makami da kai harin ramuwar gayya da satar mutane da kisan gilla da rikicin manoma da makiyaya, ya tsara yadda za a magance matsalar wadannan kalubana da suka addabi jihar.’ In ji Abutu Yaro.
Haka kazalika, jajircewa da kuma sadaukar da kai musamman ga masu munanan laifuka tare da hadin gwiwa da Gwamnatin Jiha, Sarakunan Gargajiya, Al’umma da shugabannin addinai zai taimaka wajan samun dawamamen zaman kafiya.
Kwamishina ya jaddada cewa,dole ne ‘yan sanda su kasance masu himma, masu kariya ga al’umma da warware matsaloli da tallafawa al’umma tare da basu tsaro a ko da yashe.
Ya tabbatar wa jama’a cewa ‘yan sanda karkashin kulawar sa za su sauke nauyin da ke kansu daidai da ka’idojin aikin rundunar.
Ya kuma yi gargadin cewa, ba za a amince da take hakki na dan adam ba, Kuma ba zamu aminta ta amsar cin hanci da rashawa da sauran halaye marasa kyauba.
Kwamishinan ya yi kira da a ci gaba da ba da goyon baya, hadin kai da hadin gwiwa ga kowa da kowa ta hanyar ba da bayanai masu amfani ga ‘yan sanda kan ayyukan masu aikata laifuka don daukar matakin gaggawa akan su.