Daga Lawal Umar Tilde, Jos
Sabon Kwamishinan ‘yanSanda naJihar Filato, CP Adie Jerimiah Undie, ya kama aiki.
Kamar yadda babban jam’in hulda da jama’ana rundunar ‘yan sandan Filato, ASP Tyopeb Mathias Terna, ya bayyanawa a wata takardar manema labarai da ya sanyawa hannu.
Jami’in huldan da jama’a, ya saki wannan takardar sanarwa ne a ranar Litinin din nan da ta gabata, yace sabon kwamishinan ya maye gurbin tsohon kwamishinan CP Peter Babatunde Ogunyanwo wanda aka sauya masa wurin aiki zuwa hedikwatar ‘yan sanda dake Abuja.