Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MANYAN LABARAI

Sabon Rikici Ya Ɓarke A Jam’iyyar PDP

by Tayo Adelaja
October 23, 2017
in MANYAN LABARAI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Mubarak Umar, Abuja

Ƙasa da kwana ɗaya da za gabatar da babban shugabanin jam’iyyar PDP na ƙasa (NEC), ƙungiyar zaɓaɓɓu a cikin jam’iyyar na reshen Arewa Maso Yamma, suna zargin Shugaban PDP Ahmed Makarfi da shiryawa maƙarƙashiya don yi amfani da a ƙara masa wa’adin shugabancin jam’iyyar har zuwa watan Fabrairun 2018, inda za a sahale batun filla-filla.

samndaads

A taron ganawar na PDP shugabanin ƙungiyar Arewa na shiyyar Arewa maso yamma da mambobin ƙungiyar sun bayyana cewar jam’iyyar PDP tana da kima a halin yanzu, sai suka bayyana hasashensu na lashe zaɓen 2019 da ke tafe, inda suka bayyana aniyarsu PDP na cin zaɓen na 2019 ba tare da ta’addadin faɗuwa ba, matuwar Makarfi bai kai ga yi wa jam’iyyar cin-kaca ba.

Da ya ke magana a madadin ƙungiyar a jihar Sokoto jiya, Malam Shehu Othman ya yaba da ƙoƙarin da ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP suke yi a yankin duk da kasantuwar jami’iyyar ta adawa a jihar da kuma jihohi da dama na ƙasar nan, ya kuma jinjina musu a bisa yanda suke faɗi tashinsu cikin kwanciyar hankali ba tare da matsalar ba

Haka zalika, sun kuma bayyana cewar shugaban riƙo na PDP Ahmad Makarfi yana neman kujerar shugaban ƙasa, a bisa haka suka ce sam ba za su biye masa wajen wannan ra’ayin ba.

Sun bayyana cewar yana samun goyon baya daga Sanata Ben Oni wanda kuma shi ne babban sakakatare na jam’iyyar ta ƙasa a matsayin abokin burminsa na neman kujerar shugaban ƙasa, wanda suka ce su sam ba su tare da wannan ra’ayin.

A cewar Othman, dalilin shan kayensu a zaɓen 2015 bai rasa nasaba da sakamakon sakacin shugabanin jam’iyyar na wancan lokacin suka nuna, yana mai cewar dole ne a kawo gyara don kauce wa masu neman kawo ruɗani.

“Babban dalilin da ya jawo jam’iyyarmu ta faɗi a babban zaɓen 2015 bai wuce matsalar rashin iya tafiyar da dimokraɗiyya, rashin aminci da kuma son zuciya da shugabanin jam’iyyar suka sanya a wancan lokacin ba. Matuƙar shugaban yanzu ya kai ga cimma burinsa na kayar da jam’iyyar nan, shi ke nan jam’iyyar za ta samu naƙasu ba kuma lallai mu kai ga samun mulki ba, matuƙar Makarfi ya kai ga cimma burinsa”. A cewar ƙungiyar

Ƙungiyar dai ta bayyana cewar yanzu haka ta fara tattauna gami da neman shawarwarin da wasu ‘yan yankunan na jam’iyyar domin ganin yanda za su yi da masu kawo musu koma baya a cikin harƙoƙin demokraɗiyya gami da cewa ba za su amshi wannan tsarin ba.

Ya yi ƙira da babbar murya ga shugabanin Arewa da su hanzarta zaunar da Sanata Ahmad Makarfi domin ja masa kunne da kuma hanasa kawo ruɗani da rashin fahimta a tsakaninsu.

Haka zakila, ƙungiyar ta kuma yi kira ga mabobin majalisar jam’iyyar na ƙasa da cewar su yi amfani da lokacin zaman da za su yi a ranar Talata (gobe kenan) wajen yin fatali da kuma yin watsi da dukkanin wani mummunar ra’ayi da Sanata Ahmad Makarfi yake kai da shi da ‘yan tawagarsa a tunaninsu na batun a ƙara musu wa’adi koda kuwa na rana guda ne baya ga babban taron 9 ga watan Disamba na ‘conɓention’.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Rashin Lambar BVN: Gwamnati Ta Garƙame Asusun Mutane Miliyan 15

Next Post

BAƘON MARUBUCI: Akwai Gagarumar Matsala Fa!

RelatedPosts

'Yan Adaidaita

An Sasanta Yajin Aikin ’Yan Adaidaita Bayan… Motocin ‘Kano Line’  Sun Koma Jigilar Jakara-Kasuwa

by Muhammad
6 days ago
0

Babu Hanunmu A Ciki Wannan Yaji – Shugaban ’Yan Adaidaita...

Adaidaita

Yajin Aikin Adaidaita: Acaba Ta Dawo A Kano

by Muhammad
1 week ago
0

Ya Jefa Jama’a Cikin Tsaka Mai Wuya Yadda Aka Koma...

Masu Garkuwa

Tattaunawa Da Masu Garkuwa: Yadda Gwamnonin Kaduna Da Neja Suka Raba Gari

by Muhammad
1 week ago
0

Shin Sheikh Gumi Ne Ya Raba Tsakani? Daga Nasir S....

Next Post

BAƘON MARUBUCI: Akwai Gagarumar Matsala Fa!

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version