Connect with us

KASASHEN WAJE

Sabon Rikici Ya Kara Barkewa A Sudan Ta Kudu

Published

on

A Sudan ta kudu Kwanaki kadan bayan sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka sake farfado da ita, rahotanni sun nuna cewa fadace fadace sun barke a wadansu sassan kasar, a cewar Jean Pierre Lacroid, wakilin babban sakataren MDD na musamman kan ayyukan kiyaye zaman lafiya.

Lacroid ya shaida wa wakilan kwamitin sulhu na MDD a birnin NewYork cewa “rahotanni sun nuna cewa rikici ya barke ne ne bayan da gwamnati tayi kokarin kafa shugabannin kananan hukumomi a yankunan da suke hanun ‘yan tawaye. Ya kara da cewa duka sassan biyu sun turo karin dakaru zuwa yankunan a matakin kama iko.

Ya kara da cewa rikicin na faruwa ne a jihohin Central Ekuatoria da Unity kana kuma an samu rikici sosai a cibiyar Jamula dake Mbudu a yankin Kopera.

A halin da ake ciki kuma wani rahoto da kungiyar kare hakkin Bil’Adama ta kasa da kasa Amnesty International ta fitar jiya Laraba, ta zargi sojojin gwamnti da laifin kona yara da tsoffi da ransu. An kuma yi wa mata giwa ta fadi. Tareda harbe farar hula har lahira, da bi ta kansu da motocin yaki masu sulke, ko a rataye su kan bishiyoyi ko jinka.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: