Connect with us

SIYASA

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC Ta Bauchi

Published

on

  • ‘Ya’yan APC Sun Tsige Shugaban Jam’iyyar
  • Ba Kara Zuba Jam’iyyar Take Ba, Cewar Shugaban

 

A jiya Laraba ne wani sabon rigima da rikici ya kunno kai a cikin jam’iyyar APC reshen jihar Bauchi, inda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka sanar da dakatarwa tare da tsige Uba Ahmad Nana a matsayin shugaban jam’iyyar a matakin jihar.

Bayan da suka tsige shi, shi kuma Uba Nana ya ce jam’iyyar ai ba kara zube take ba, yana mai cewa tana tafiya ne bisa dokoki da ka’idoji.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin taron manema labaru da wasu ‘ya’yan APC din suka kira a ofishin jam’iyyar APC da ke Turum ,suna masu shaida cewar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar shine ya jagoranci aiwatar da haramtacen zaben shugabanin jam’iyyar a matakin jihar da ya kai ga kawo baraka da rashin amincewar wasu bangaren, don haka ne a yanzu suka sanar da dakatar da Uba Nana a matsayin shugaban jam’iyyar kwata-kwata.

Da ya ke magana da ‘yan jarida a madadin mambobin jam’iyyar APC gaba daya, wakilin jam’iyyar a matakin kasa kuma jigo a jam’iyyar a matakin jihar, Alhaji Ibrahim Ago, ya shaida cewar sun dauki matakin ne domin dawo da bartaba da kimar jam’iyyar, yana mai cewa zaben da ya kai ga ayyana Uba Nana a matsayin shugaban jam’iyyar haramtacce ne.

Ya ce, zaben da aka yi a 2018 har Uba Nana ya zarce a matsayin shugaban APC haramtacce ne, “Ba wanda zai sake kiran kansa shugaban jam’iyya har san an zo an sake yin zabe.  Muna son jama’a su sani shugaban da ya ke kiran kansa shugaban APC (Uba Ahmad Nana) ba shugaba bane,”

Ya ce sun sanya shugaban riko da zai jagoranci jam’iyyar har zuwa a sake yin zabe, “Shugaban APC na riko yanzu a jihar Bauchi shine Malam Aminu Na-Borno, shugaban APC na karamar hukumar Shira shine sabon shugaban APC na riko,” A fadin Ago.

Ibrahim Ago ya kuma shaida cewar, “Mun so tun lokacin da aka yi zaben shugabanin jam’iyyar mu daidaito da badakalar da aka yi. Amma a sakamakon gwanatin baya a lokacin ta yi kaka-gida cikin lamarin hakan ya gagara.

“Muddin ana son APC ta gyaru dole ne sai Uba Ahmad Nana ya sauka. Akwai kudaden jam’iyyar nan ba mu san inda ya ke kaisu ba, dole ne kawai sai ya sauka,” A cewar shi.

Daga nan sun zargi Uba Nana da hada kai da gwamnati mai ci a lokacin zaben 2019 da har hakan ya kai ga shan kayen APC a jihar, ya kuma sake zarginshi da cewar har yanzu yana da alaka da gwamantin PDP mai ci a jihar.

“Muna zarginsa da hada kai da gwamnati mai ci har ya kai ga jawo faduwar jam’iyyarmu a jihar Bauchi,” A cewar Jigon.

Shi ma Alhaji Rabi’u Shehu Dan-Baba, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a matakin karamar hukumar Bauchi, ya shaida cewar jam’iyyar APC ta kasa cigaba a kullum matsaloli su ke samu a sakamakon gazawar Uba Nana, ya kuma ce rashin adalci da rashin iya shugabanci sun mamaye jam’iyyar don haka sun dakatar da shi har zuwa lokacin da za a sake zabe.

Da ya ke mai martani kan wadannan batutuwan, shugaban jam’iyyar APC na jihar Bauchi, Alhaji Uba Ahmad Nana, ya shaida cewar jam’iyyar APC jam’iyyace da take tafiya bisa tsari da dokokinta, don haka ya shaida cewar duk abin da wadannan fusatattun mambobin jam’iyyar su ke yi bai bisa ka’ida.

Da ya ke ganawa da manema labaru Uba Nan ya ce, an zabeshi a matsayin shugaba kuma yana kan kujerarsa ta shugaba, ya shaida cewar dukkanin matakan da suka dace jam’iyya ta tafiya a kai, APC ma tana tafiya a kai.

Ya ce, mambobin da su ke wannan ikirarin an sake zabe basu samu nasarar kaiwa ga zarcewa a a matsayin shugabannin jam’iyyar ba, “Wannan dalilin ya sanya suka fusata,” sai dai ya shaida cewar abun da su ke yi bai ma kai jam’iyya da kanta ta tsaya biye musu ba.

“Kungiyoyi irinsu za su basu amsa daidai da abubuwan da suka yi,” A cewar Uba Ahmad Nana.

“Kowa ya san yadda ake sauke shugaba a bisa doka da ka’ida, amma haka siddan wasu fusatattu su ce sun dakatar da shugaban wannan ya zama hauragiya.

“Da su shugaban APC ne a matakin karamar hukuma, da aka sake yin zaben shugabanni Allah bai sanya sun samu nasarar komawa ba. Don haka basu da wata matsayi a jam’iyyar APC kwata-kwata,” A cewar Uba Nana.
Advertisement

labarai