Umar Muhsin Ciroma" />

Sabon Salon Dafa Kayataccen Dambun shinkafa

Duk da kasancewar shinkafa tuni ta zama abinci na yau da kullum kuma gama garin abincin da kowane gida sai ka ganta, amma idan uwargida ta san kanta da kyau za ta iya sarrafa shinkafa ta yadda za ta fitar da dahuwa da za ta ja ra’ayin iyalin gida wajen cin abin da ta girka.

Yana da matukar kyau a ce uwargida tana da nau’o’in abinci kala daban-daban ta yadda ba za ta gundiri maigida da yaranta da nau’in abinci daya zuwa biyu ba.

A saboda haka DAMBUN SHINKAFA na daya daga cikin nau’in girke-girken da uwargida ya kamata ta kara a taskarta ta girke-girke.

Kayan hadi:

– Shinkafa

– Karas

– Koren wake

– kabeji

– albasa

– attaruhu

– Sinadarin dandano

– gishiri

– hanta

– man gyada

Yadda ake hadawa:

Da farko dai  za ki samu shinkafarki iya adadin da kike bukata, ki kai a barzo miki. Ki fid da garin ta hanyar tankadewa ki dauki tsakin ki wanke shi tas! Ki zuba amadanbaci, ki rufe ruf da leda sannan ki dord a wuta ki kawo murfi ki rufe don ba a so tiririn ya dinga fita. Ki tabbatar kin zuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda ba zai kone ba.

Ki tafasa karas dinki sama-sama. Ba lugub ba, ki yayyanka shi bayan kin kankare bayan. Shi ma koren waken ki tafasa shi, akwai wanda ake siyarwa bararre kuma busasshe to da shi za ki amfani. Kabejin ma ki wanke shi tas ki yanka amma ba kanana can ba.

Attaruhu da albasa ki yankasu su ma yadda ki ke bukata. Ana so albasar ta yi yawa. Hantarki ki tafasa da isasshen sinadarin dandano da dan gishiri, ki yanka gutsi-gutsi. Bayan tsakinki ya yi laushi sai ki sauke ki zuba mai ya kama shi, sannan ki kawo kayan lambun nan ki zuba, ki cakuda su yadda za su hade jikinsu da tsakin haka ma attarugu da albasar nan hade da yankakken hantar nan ki hada ki sake juyawa, sannan ki dan saka sinadarin dandano da gishiri kadan yadda ba zai yi yawa ba, ki cakuda, ki mayar wuta.

Ki ba shi lokaci za ki ji yana fid da kamshi sosai, ki tabbatar ya yi kamshi kuma ya dahu sosai yadda ake so, ki sauke. Za a iya ci a haka, ko kuma ki yi masa miyar kayan lambu.

Yadda Ake Yin Miyar Kwai

Abubuwan hadawa

Kwai

Tarugu

Albasa

Kori da Tem

Garin citta kadan

Koren tattasai

Koren wake

Karas

Bota

Knor chicken ko Maggi chicken (ya danganta da irin dandanonki)

Yadda ake hadawa

1. Da farko za ki fasa kwanki  ciki wani karamin kwano, sai ki yanka albasa a ciki, ki ajiye a gefe.

2. Ki wanke ki cire dattin bayan karas dinki, ki wanke su koren wake ,albasa da tarugunki, sai ki yanka su dogo-dogo, bayan kin gama sai ki dauko kasar din da koren wake, ki sa musu ruwan zafi sosai (tafasashshe), sai ki sa baking powder ko kanwa a ciki ki rufe shi na dan wani lokaci, sai ki cire shi cikin ruwan sannan ki sake wanke shi ki tsane shi, sannan ki ajiye a gefe.

3. Ki dora tukunyarki a kan wuta ki sa bota kadan ki narka, sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soya sama-sama.

4. Ki dauko yankakken tarugunki ki sa a ciki da su maggi , garin citta kadan, curry da thyme sai ki kawo ruwan zafi kadan sai ki juya ki rufe shi na dan wani lokaci.

5. Sai ki dauko kwanki (wanda ki ka fasa a kwano) ki zuba cikin tukunya ki dake kan wuta ki rufe ki barshi nadan wani lokaci.

6. ki rage wuta sai ki bude ki kawo su carrot, koren wake ki sa sai ki juya shi a hankali ki kara rufeshi nadan wani lokaci har sai ruwan ciki ya shanye, sai ki sauke

za ki iya ci da soyayyen dankalin turawa ko doya. A ci dadi lafiya

“KUNUN ‘YA’YAN ITACE“

Kayan Hadi

Garin Alkama ko semo ko shinkafa

Ayaba

Kankana

Abarba

Tuffa

Kwakwa

Yadda Ake Hadawa

Da farko za ki goga kwakwarki ki zuba ruwa ki tafasa kar ki tace garin tsakin kwakwar idan ruwan ya tafasa sai ki hada garin da ruwan sanyi ki kwara tafashshen ruwan a kai ki dama kunun. Dama kin yanka ya ‘yan ita ce kanana daga nan saiki zuba a kan kunun, kisa suga da madara wannan kunu yana da dadi sosai za ki iya yi wa mai gida tare da alalan kabeji.

Exit mobile version