Sabon Salon Tuggu Da Manakisa Ta Hanyar Jinkiri

A ranar 21 ga watan Yuni 2018 ne alkalin wata kotu mai zama a Kaduna ya ki bayyana alhali kotu ta sanya cewa akwai zama a ranar, bisa uzurin jita-jitar wai hatsari ya samu sakamakon buge shi da mai Keke-Napep ya yi. Lamarin ya yi matukar ba mutane kamar ni mamaki, wadanda ke zaman jiran zuwan wannan rana tare da burin zuwan karshen wani lamari da ya ki ci, ya ki cinye wa, har na tsawon shekaru uku. A maimakon a matsar da ranar sauraron karar zuwa 11 ga watan Yuli. Ko ba komi yanayin yadda lamurran ke tafiya suna kara tabbatar da zargin da ake da shi akan gabadaya lamarin ne.
Kamar yadda aka sani, Mahaifina da Mahaifiyata da wasu mutum biyu wai ana zarginsu ne da aikata laifin kashe wani Kofur din Soja a watan Disambar shekarar 2015, a ranakun da Sojojin Nijeriya suka kashe daruruwan maza da mata, ciki har da kananan yara. Wannan ita ce dai tuhumar da ake yi wa sama da mutum 100 da ke garkame a gidan yari; wadanda ba a san ranar da za a kawo karshen wannan tsarewa da ake yi musu ba.
Yana da kyau a fahimci cewa a baya a watan Afrilu lokacin da kotu ta zauna kan batun, an dage karar saboda ikirarin da lauyan mai shigar da kara yayi na cewa ba su iya riskar biyu daga cikin wadanda ake kara ba – zancen da a kashin kansa karya ne. Zancen gaskiya shi ne babu daya daga cikin mutum biyun da ya gudu, an san adireshinsu da wuraren da za a same su. Babu wani kokari da aka gwada na ba su sammaci balle a ga ko za su amsa gayyatar. Har zuwa yanzu da nake rubutun nan, babu daya daga cikinsu da aka aike wa da takardar sammaci. kuma babu wata alama da ke nuni da cewa za a aike musu da takardar. Alamu na nuna da gangan Gwamnati take aikata wadannan abubuwa don ta kara bata lokaci, ta hanyar yin amfani da duk wasu dabarun bata lokaci ta yadda za su ci gaba da tsare Mahaifana har rashin lafiya ya yi ajalinsu. Wannan na daga cikin dalilan da za su sa dole a yi wa mutum uzuri idan ya ce, hatsarin da ake cewa ya samu alkalin nan kirkirarren zance ne.
A daya bangaren labarin kuma, sai ga labarin hargitsi a titunan Kaduna. sama da shekaru biyu kenan yanzu, Sojoji da ‘yan sanda ko zauna gari banza da aka yo hayarsu suna afkawa jerin gwanon mu na lumana. Wadannan hare-hare sun yi ta zama sanadin salwantar rayukan mutane maza, mata da yaran da ba su ji ba, ba su gani ba. Irin wannan ya afku a Babban Birnin Tarayya Abuja, ya kuma afku a Kaduna da sauran wurare. A ‘yan kwanakin nan da suka gabata lamarin ya kara kamari. Da farko a wata sanarwa da Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Kaduna ta fitar a ranar 20 ga watan Yuni, 2018, sun bayyana cewa; ‘Yan Shi’a za su haifar da tarzoma da gangan a Kaduna, sun bayyana cewa, wadannan ‘yan Shi’ar wadanda suka yi wa lakabi da masu tada zaune tsaye za su fito dauke da bindigu, wukake, da Bama-Bamai da wasu karin muggan makamai. Haka kuwa aka yi, Muzaharar lumanar da aka saba gudanarwa sama da watanni biyu a Kaduna sai ya zama jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun auka mata. Harin mummuna ne me hatsari.
Sai dai bambancin da aka samu a wannan lokacin, cikin wadanda suka samu rauni har da jami’an tsaro. Abin da har yanzun ban gama tantancewa ba shi ne, shin wadanda suka aukar da wannan barna Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya reshen Jihar Kaduna ne, ko kuma zauna gari banza da gwamnatin el-Rufai ta dauki hayarsu kuma yake amfani da su akan abokan hamayyarsa ta siyasa.
Sanin kowa ne cewa an rushe gidajenmu, an yi wa ‘yancinmu hawan kawara, an yiwa ‘yan uwanmu kisan gilla ba tare da an bamu damar yi musu jana’iza kamar yadda addini ya tanada ba, amma duk da wadannan mun ci gaba da kasancewa cikin nizami, kuma za mu ci gaba da kasancewa a haka. Ni da kaina na taba fadin cewa, a matsayina na dan kasa mai bin dokokin kasa, zan iya bayyana a kowanne ofishi, na yi rantsuwa cewa zan bi duk wata hanya da ta dace don ganin iyayena sun samu lafiya, a rantsuwar tawa na yi nuni da cewa ba zan taba bin hanyoyin hayaniya ba; kuma da izinin Allah har zuwa yau ban sauka daga kan wannan ba. Haka kuma na rantse cewa zan yi amfani da ‘yancin da nake da shi a matsayina na dan kasa wurin yin zabe a shekarar 2019, kuma ina mai tabbatar da cewa ba ni kadai ne akan wannan matsayar ba.
Jam’iyyar APC wacce mu al’umma muka zaba har ta dare kan karagar mulki, a tsawon shekaru ukun da ta yi ta tabbatar da cewa ita makiyar al’umma ce. A karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari, an azabtar da duk wani mutumin da ya ki lankwasuwa ga son ran dandazon ‘yan korensa. A maimakon a samar da tsaro ga duk dan kasa, sai ya kasance wannan gwamnatin ta na amfani da munanan hanyoyin aikata barna kan al’umma. Wannan karfin shaidana da ta suke da ita a yanzu ne suke amfani da ita wurin murkushe duk wani wanda ya ki bin son ransu. Wannan ya fi kamari a Jihar Kaduna, inda wani Bakwaini da ake kira Nasiru el-Rufai ya tabbatarwa duniya cewa shi ba ya aiki da hankali, makiyi ne na zaman lafiya, makiyi ne na doka kuma makiyin ka’ida.Abin mamaki da har ya iya rufe ido wurin yin amfani da zauna gari banzansa wurin afkawa ‘yan sanda. Don dai kawai ya tabbatarwa da mutane wai ‘yan Shi’a ‘yan tada kayar baya ne. Kamar dai Chukwuma, bai ki ya ci gaba da daukar alhakin tura mutane zuwa kaburburansu ba, tamkar kuma Attila, babban burinsa shi ne ya yi dalar kawunan mutane a saman gidajensu da ofisoshinsu a fadin jihar.
Zan sake nanatawa, a shekarar 2019, matukar za a gudanar da zaben gaskiya da gaskiya, shi ko ubangidansa babu wanda zai iya lashe sahihin zabe. Idan zuwa lokacin sun iya nasarar aiwatar da ta’addancinsu na kisa, hart a kai mutane da dama sun sallama mutuncinsu, toh Allah ya jikan wadanda suka yi saura kawai za a ce.
Ina jajantawa iyalin wadanda aka kashe da wadanda aka yi wa rauni, ciki kuwa har da iyalin dan sandan da gawarsa ta cike ko ina a kafafen sadarwa. Jami’in tsaron kasa dake aiwatar da aikinsa kamar yadda doka ta tanada bai cancanci irin wannan danyen hukunci ba.
Haka shi ma mai burin zama Injiniyan Jirgin Sama, ko Injiniyan Sinadarai, ko kwararren Mai zane, da Kwararren Masanin Halayyar Dan Adam, ko Humaid (Kanina) Yaro dan Makaranta mai shekaru 14 duk ba su cancaci danyen aikin kisan gilla ba.
Ina shawartan abokaina da ke cikin ‘yan sanda da su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda doka ta tanada, kuma su sa a ransu cewa el-Rufai da ya aikata wannan danyen aiki, mahakin Kabarin baidaya kuma makashi, zai fuskanci sakamakon ayyukansa kamar sauran makasa.

Mohammed Ibraheem Zakzaky, ya rubuto Daga Zariya, Jihar Kaduna
Imel: Mz4real1@gmail.com

Exit mobile version