Sabon Salon Wayar IPhone 13

IPhone 13

Daga Ibrahim Sabo,

Kamfanin Apple ya sanar da sabon samfurin wayarsa ta iPhone 13, wacce za ta iya daukar faifen bidiyon ‘Hoton fuska’ mai cikakken fasali, wanda hakan ke nufin wani bangare na hoton da abin da ka dauka zai kasance ya fita fes, sannan sauran bangarorin kamar na baya da kuma gefensa za su kasance dushi-dushi.

Sabon yanayin daukar bidiyo ‘na nuna yadda wani ke shirin shiga cikin bangon kewayen hoton’ sannan ya kan mayar da hankali a kan su, in ji kamfanin Apple din. Wani abu da ake kira ”mayar da daukacin hankali kan abu”.

Ita kadai ce wayar tafi-da-gidanka da za ta bai wa masu amfani da ita damar yin gyare-gyare da kwaskwarima bayan daukar hoton, jagoran kamfanin na Apple, Tim Cook ne ya bayyana hakan.

Amma kuma, akasarin sauran abubuwan da sabuwar samfurin wayar ta kunsa an kara sabunta ne daga samufurinta na baya.

Haka kuma labarai game da abin da ya shafi sirri a tattare da wayoyin kamfanin na Apple wanda ka iya bankada sakonnin kar-ta-kwana na masu amfani da wayoyin sun kanka ne wannan sabon batu.

A ranar Litinin ne kamfanin na Apple ya fitar da wani tsari na tsaro ga abin da aka bayyana a baya wanda bata san da shi ba wanda zai bai wa masu kutse damar shiga cikin bangaren sakonnin kar-ta-kwana ba tare da mai amfani da wayar ya latsa a kan layin da zai bude musu wani shafi ba ko kuma kundi.

Sabuwar iPhone din ta kunshi guntun karfe mai sauri na A15, da kuma fuska mafi haske, da karfin batirin da zai kai tsawon sa’o’i biyu da rabi. Sannan ta zo da sabbin launuka da suka hada da ruwan hoda, da shudi, da ja, da baki da kuma fari.

Sabuwar wayar ta iPhone 13, tana kuma da ma’ajiya mai daukar nauyin gigabayit 500 (500GB) wanda mafi karancin ma’ajiyarta ke kai wa har 128 gigabayit (128GB) idan aka kwatanta da samfurin irinta na baya masu nauyin 64 gigabayit (64GB) kawai.

Apple ya kuma bugi kirjin nuna goyon bayansa wajen kare muhalli, yana mai cewa an sarrafa wayar da kayayyaki da dama da aka gama amfani da su, da suka hada da wayoyin yankin da aka sarrafa daga robobin ruwan sha.
kaddamarwar na zuwa ne a lokacin da masu sayen ke ci gaba da barin wayoyinsu na kai wa tsawon lokaci kafin su kara inganta su.

Kamfanin zuba jari na ‘Wedbush Securities’ ya kididdige cewa masu amfani da wayoyin na iPhone kusan miliyan dari biyu da hamsin ne basu inganta wayoyin na su ba har na tsawon shekaru uku da rabi.

Paolo Pescatore, wani mai sharhi ne a hukumar ‘PP Foresight’ da ya bayyana cewa da dama har yanzu ba su samu amfana da sabbin fasalin wayoyi na zamani ba.

“A lokacin da, da dama za su dauki inganta wayoyin a matsayin karuwa, akwai miliyoyin masu amfani da wayoyin da har yanzu ba su inganta su zuwa fasahar intanet ta 5G ba,” inji shi.

Ana iya amfani da fasahar intanet ta 5G ne kawai a kan samfurin wayar iPhone 12, wacce aka fitar cikin shekarar da ta gabata, da kuma sabbin samfurin da aka sanar.

A cikin watanni ukun tsakiyar wannan shekarar, kamfanin Apple ya sayar da kusan kashi uku bisa dari (25.9%) na duka wayoyinsa masu amfani da fasahar intanet ta 5G a fadin duniya, kamar yadda kamfanin IDC,  ya bayyana.

Marta Pinto, babban manajan bincike a kamfanin na IDC ya ce: “Da wannan sabon matsayi, wadannan alkaluma za su karu tare da kara karfi wajen maye gurbin mamayar da kamfanin Apple ya yi a wancan gurbin.”
Shi ma kamfanin Apple ya kaddamar da samfurin kananan wayoyi na iPhone 13 Mini, da Pro da kuma Pro Max.

Samufurin wayoyin iPhone 13, da Pro da kuma Pro Mad na kunshe da kyamarori uku kuma wanda Apple din ke kira “tsarin kyamara mafi inganci a yanzu”.

Kudin samfurin wayoyin iPhone 13 mini ya fara daga Fan dari shida da saba’in da bakwai (£679), yayin da iPhone 13 ya fara daga Fan dari bakwai da saba’in da tara (£779).

Samfurin iPhone 13 Pro ita kuma kudin ta ya fara daga Fan dari tara da arba’in da tara, sannan mafi girma samfurin Pro Mad ita kuma Fan dubu daya da arba’in da tara (£1,049).

Ana daukaka kamfanin Apple wajen kirkirar sabuwar fasaha. Amma muddin wannan kaddamarwa ta kasancewa wani abu na daban, wannan daukaka ta zama tsohon ya yi.

Babu wani sabon abu ko na musamman da aka sanar a nan. kara sabunta wayoyinsa na iPhone, da Apple Watch da kuma iPad ya zama wani abu da aka saba gani, da rashin bayar da sha’awa, da kuma kariya.

Inganta sabon tsarin kyamara mai daukar bidiyo (wanda a kashin gaskiya ya yi kyau) sake sabunta na baya ne.
Ita kan ta gabatarwar, duk da cewa cikin sauki ne, amma babu takamaimen abubuwan da musamman ko na wata basira da za a rika tunawa da su a ciki.

Jita-jita game da kara inganta wasu abubuwan armashi, kamar misali wayoyin iPhones masu iya amfani da tauraron dan adam, duk daga karshe sun zama shaci-fadi.

“Wannan wata gagarumar sanarwa ce,” in ji shugaban kamfanin na Apple Tim Cook, yana danganta wa da kayayyaki kamar su sabuwar wayar iPhone 13, wacce ta ke kusan kama da samfurin iPhone 12″
Wasu na rade-radin cewa mai yiwuwa kamfanin na Apple zai daina lakaba wa samfurin wayoyinsa lambobi (kasancewar lamba 13 rashin sa’a ce ga wasu) amma babu wani yunkuri mai kama da haka.

Ka yi tunanin da ya wuce batun gagarumin kiran kasuwar kana wanda ya kasance kaddamarwar da bata bayar da sha’awa ba, musamman ma daga kamfanin da ke son bayyana kan sa a matsayin mai basirar fito da sabuwar fasaha.

Exit mobile version