Ibrahim Muhammad" />

Sabon Sarkin Kano Ya Fara Aiki Da Ziyartar Firamaren Gidan Makama

Mai martaba sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ziyarci Makarantar Firamare ta gidan Makama da ke dab da Fadar Masarautar Kano a matsayin aikinsa na farko bayan da Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya mika masa takardar kama aiki a matsayinsa na Sarkin Kano na 16 a Daular Fulani tare da dan uwansa, Mai Martaba Alhaji Nasiru Ado Bayero, a matsayin sabon Sarkin Bichi na biyu a tarihin sabuwar Masarautar ta Bichi a ranar Larabar da ta gabata.

Bayan da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya isa Fadarsa da ke Kofar Kudu a gidan Sarkin Kano bayan Almuru, wayewar garin Alhamis ke da wuya kuma, sai Sarkin Kano ya fito tare da tawagarsa zuwa Makarantar Firamare ta gidan makama, inda bayanai suka  nuna cewa shi ma Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero Mahaifi ga sabon Sarkin Kanon na yanzu, da wannan makaranta ta gidan Makama ya fara nasa aikin kamar yadda tarihi ya nuna.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nuna farin cikinsa tare da gode wa Allah (SWT) da ya ba shi damar yin wannan ziyara, sannan kuma ya sha alwashin taimakawa ilimi da kuma dukkanin sauran wasu abubuwan alhairi wadanda za su taimakawa Jihar Kano da Kanawa a iya tsawon rayuwarsa a matsayinsa na Sarkin Kano.
Injiniya Babangida Lamido, shi ne jagoran tsofaffin dalibai na Makarantar Gidan Makama, wanda ya jagoranci karbar tawagar sabon Sarkin, tare da mika kokensa a madadin tsofaffin daliban makarantar cewa, wannan makaranta ta Firamare duk da kasancewar an karbi aron wani bangare nata da aka mayar da shi Sakandire, wanda aka yi alkawarin dawo da shi a dan wani kankanin lokaci, amma ga shi yau an dauki tsawon lokaci ba a dawo da shi ba, duk  da yanzu dai an sake sanya watanni shida a matsayin lokacin da za a dawo da shi.
Hajiya Sadiya Tahir, Shugabar Makarantar Firamare ta Gidan na Makama ta yi matukar nuna farin cikinta akan wannan ziya ta Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ga wannan makaranta ta Gidan Makama a Kano a matsayin abin alfahari da godiya ga Allah da kuma mai martaba Sarkin na Kano.
Haka zalika, Ita ma Shugabar Makarantar Sakandire ta Gidan Makama ta ce, makarantar yanzu ta tashi daga karamar Sakandire zuwa babbar Sakandire a 2017, sannan zuwan Sarkin Kano wannan wuri ko shakka babu babban alhairi ne ga makarantun da ma Jihar Kano baki-daya. Kazalika, ita ma ta mika bukatar makarantar na rashin kayayyakin aiki da makarantar ke fama da shi, wadanda suka hada da kujeru da sauran makamantansu.

Exit mobile version