Connect with us

MANYAN LABARAI

Sabon Sarkin Kano Ya Yi Magana Karon Farko

Published

on

…Kan Annobar Korona Da Mace-macen Kano

A karon farko tun bayan barkewar annobar cutar Korona, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bara kan batun, inda ya yi magana, musamman kan halin da kasarsa ta Kano ke ciki.

Sarkin, wanda ya yi magana a wani sakon bidiyo a jiya ga Kanawa, ya ce, ma’aikatar lafiya ta jihar ta sanar da shi cewa, a na cigaba da samun bullar cutar ta Korona a jihar da kuma wasu mace-mace da a ke faman samua birnin Kano, to amma ma’aikatar ta tabbatar ma sa da cewa, yawaitar mutuwar ba shi da alaka da cutar ta Korona.
Ga cikakken jawabin na Mai Martaba Sarki Aminu Bayero:
“A’uzu billahi minal shaidanin rajim bismillahi rahmani Rahim, wa sallallahu alannabiyil kareem. Jama’a assalamu alaikum.
“Ma’aikatar lafiya ta jiha ta sanar da mu rahoton ci gaba da samun bullar cobid 19 a sassan wannan jaha. Kuma wannan rahoto na da matukar jan hankali sosai, rahoton ya kara tabatar mana da cewa cobid 19 gaskiya ce, kuma kimanin mutane saba’in da uku ne a yanzu aka tabbatar sun kamu da wannan cuta a wannan jaha.
“Jama’a dangane da wannan halin da muke ciki ya zama wajibi a gare mu, da mu kara kira ga jama’armu a kiyaye da wadannan matakai domin dakile ci gaban yaduwar wannan cuta tsakanin al’umma. Lallai jama’a su killace kawunansu kamar yadda gwamnati ta yi umarni, su guji shiga cunkoso tare da nisantar hirarraki a majalisu da sauran wuraren hira. Jama’a su ci gaba da wanke hannayensu a ko da yaushe da sabulu da ruwa mai gudana tare da amfani da takunkumin rufe hanci da baki.
“Iyaye da sauran shuwagabanni na al’umma su sa ido sosai akan yaranmu tare da hana su yin wasannin kwallo domi hana cudanya tsakaninsu. Jama’a su guji nuna kyama ga wadandda ake zaton na dauke da cutar domin yin haka zai taimaka wajen yaduwarta tsakani al’umma. Haka jama’a su guji yada jita-jita na labarai marassa tushe da za su tada hankalin al’umma.
“Da zarar an samu mai dauke da alamomin wannan cuta ta covid 19 a sanar da ma’aikatan lafiya ta hanyar lambobin da ka yi tanadi. Muna kira ga jama’a su ci gaba da addu’a da kwantar da hankalinsu domin hukumomin lafiya da gwamnati na tsaye domin ganin an shawo kan wannan annoba.
“Za mu dau wanna dama mu yi wa al’umma ta’aziyyar rashe-rashe da a ka samu a wannan gari namu wanda jami’an lafiya sun sanar da mu ba dalilin wannan annoba ta Covid 19 ba ne. Allah ya yafe musu kurakuransu Allah ya sa suna aljannar fiddausi. Allah mu ma ya yafe ma na kurakuranmu albarkar wannan wata, ya kuma karbi ibadarmu.
“Wadanda suka kamu da wannan ciwo ya ba su lafiya, Allah ya ci gaba da kiyaye wadanda ba su kamu ba. Allah ya kare mutuncinmu da addininmu Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya. Iyayenmu da malumanmu da shuwaganninmu da suka koma ga ubangiji Allah ya jaddada musu rahma, Allah ya ba mu albarkacinsu idan wa’adinmu ya yi Allah ya sa mu cika da Imani. Assalamu alaikum.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: