Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa za ta fara wani sabon shiri na koyar da tsoffin ƴan bindiga da suka miƙa wuya, domin sauya musu tunani da kuma koyar da su sana’o’in dogaro da kai.
Shirin, wanda hukumar ilimin manya ta jihar ke jagoranta, zai haɗa da buɗe azuzuwa na karatun boko da na addini, da kuma darussa na faɗakarwa kan illolin kashe mutane da neman fansa.
- Hada-hadar Tattalin Arzikin Sin Ta Gudana Bisa Daidaito A Watan Mayu
- Hada-hadar Tattalin Arzikin Sin Ta Gudana Bisa Daidaito A Watan Mayu
Daraktar hukumar ilimin manya ta jihar, Bilkisu Muhammad Kakai, ta shaida wa manema cewa nan ba da jimawa ba za a fara aikawa da malamai zuwa ƙananan hukumomi domin koyar da waɗanda suka tuba.
Ta ce, shirin yana da nufin gyara tunanin waɗannan matasa da suka shiga harkar ta’addanci, tare da tallafa musu su koma cikin al’umma cikin mutunci da rayuwa mai kyau.
Sai dai masana tsaro sun ce shirin ba zai yi tasiri sosai ba idan ba a kula da waɗanda aka cuta da hare-haren ba.
Sun bayyana cewa akwai hatsarin ganin wasu daga cikin waɗanda suka tuba su koma yin laifi, idan gwamnati ba ta yi hattara ba.
Sun kuma jaddada cewa dole ne a tallafa wa iyalan da suka rasa ‘yan uwa da dukiyoyinsu a harin ‘yan bindiga, domin ka da su ji kamar gwamnati na goyon bayan masu laifi.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, wanda ya haddasa mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiya.