Daga El-Mansur Abubakar,
Sabon zababben shugaban karamar hukumar Akko a Jihar Gombe, Alhaji Abubakar Usman Barambu, ya dauki aniyar cika alkawuran da ya dauka a lokacin zabe da cewa idan aka zabe shi zai samar da ayyukan raya kasa da kuma inganta harkar Ilimi a karamar hukumar inda yanzu tuni al’ummar Akko sun fara gani a kasa.
Alhaji Abubakar Barambu a cikin hirarsa da Wakilin LEADERSHIP A YAU na Jihar Gombe ya bayyana cewa, daga shigar sa ofis a ranar 20 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ya fara zaga illahirin yankin karamar hukumar dan ganin ta inda zai fara inda a makon jiya ya ziyarci garin Mai Ganga inda kamfanin siminti na Ashaka suke daukar gawayi dan sabunta yarjejeniyar kudin shigar da suke biya.
Yace a lokacin da yaje Mai Ganga shugaban kamfanin simintin na Ashaka ya yi alkawarin za su zauna da shugaban karamar hukumar dan fahimtar juna saboda suna kyakkyawar fahimta mutanen karamar hukumar Akko.
Yace yanzu haka ya bada umurnin a nemo rijiyoyin burtsatse wato bohul guda biyar a kowacce mazaba biyar cikin mazabu goma sha biyar da ake dasu suka lalace dan a gyara musu saboda su sami ruwan sha mai tsafta
Ya kara da cewa zai bai wa harkar Ilimi ma fifiko sannan yace zai farfado da harkar kiwon lafiya domin wasu cibiyoyin lafiya magani suke nema wasu gyara sannan an dauki Mata da dama masu kula da haihuwa dan ganin bai dace ace Namiji ne zai karbi haihuwar Mace ba a lokacin da take kokarin haihuwa.
Alhaji Abubakar Barambu, ya kuma tabbatarwa da jama’ar karamar hukumar Akko cewa in sha Allah za su ga aiki a kasa kamar yadda ya yi alkawari a lokacin da ya zo neman kuri’un su kuma shi ba aikin ganin ido zai yi aiki nagari ingattacce.
Yace kamar yadda gwamnan sa Muhammadu Inuwa Yahaya, ya zama gwamnan aiki a Najeriya shi ma zai shiga rigar sa ya dinga kamantawa jama’ar karamar hukumar da suka zabe shi saboda yardarm da suka yi suka zabe shi da nufin zai musu aiki.
Barambu, ya yi amfani da wannan damar ya yi kira ga daukacin al’ummar Akko manya da kanana da cewa duk wani abu na al’umma da suke ganin ya dace ayi su sanar dashi zai ga yadda za a yi a yi shi idan bai fi karfinsa ba.
Daga nan sai ya godewa gwamna Inuwa Yahaya na bude musu kofa da yayi su sameshi akan duk wani aiki da suke neman ayi musu da yafi karfin su inda yace suma shugabanin kananan hukumomi za su ci gaba da bashi duk wani hadin kai da goyon baya da yake bukata.