Khalid Idris Doya" />

Sabon Shugaban SUBEB Ya Kama Aiki Da Shan Alwashin Bai Wa Marar Da Kunya

Sabon shugaban hukumar ilimin bai-daya na jihar Bauchi (SUBEB), Dakta Abubakar Surumbai, dan fitattaccen Malamin Darikan nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kama aiki a matsayin shugaban hukumar da shan alwashin yin aiki tukuro domin daukaka darajar ilimi.

Da yake jawabi a wajen bikin kama aiki da aka shirya masa a cikin makon nan, Sumrubai, ya kuma sha alwashin cewar zai yi aiki tukuro domin tabbatar da rage yawan yara maza da mata da basu zuwa makaranta a jihar ta Bauchi, ya kuma kara da jaddada cewar zai bayar da gagarumin fifiko wajen kyautata harkar ilimi a makarantun Firamare da sakandari da suke jihar.

Dakta Abubakar ya roki dukkanin manya da kananan ma’aikatan hukumar wajen yin aiki kafada-kafada domin cimma nasarar da aka sanya a gaba, “jihar Bauchi ita ce samar da Firaministan Nijeriya na farko, amma kuma yanzu jihar ta zama na gaba-gaba wajen fama da yaran da basu zuwa makaranta wannan abun damuwa ne.

“Muna neman goyon bayan sarakuna, shugabannin addinai, da masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da shawo kan matsalar yara da basu zuwa makaranta a wannan jihar domin cin gajiyar ilimi da ci gaba,” A cewar shi.

Surumbai, ya kuma sha alwashin cewar hukumar a karkashinsa za ta yi aiki da dukkanin masu ruwa da tsaki wajen samar da ilimi mai nagarta tun daga matakin farko hadi da tabbatar da yara suna zuwa makaranta a kowani lungu da sako na jihar.

Surumbai ya ce a cikin muradinsa na tabbatar da dawo da martabar aiki, zai ke kai ziyarar bazata zuwa makarantu domin tabbatar da malamai suna shiga aji don koyar da dalibai darasi a kan lokaci gami da kuma koyar da ababen da suka dace, ya hori malamai kan sakaci da aiki, yana mai cewa ba zai lamunci hakan ba.

“Muna son samar da ilimi mai nagarta, ba za mu tsaya a kan matsayin da muke ji na halin da makarantun firamare ke ciki ba, dole ne mu tashi tsaye wajen tabbatar da shawo kan matsalolin da suke akwai,” A cewar shi.

Shugaban ya kuma nemi hadin kai jama’a domin tabbatar da nasara, “ina mai nuna godiyata wa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad a bisa nadina da yayi a wannan kujerar, ina mai tabbatar masa zan yi aiki sosai wajen shawo kan matsalolin ilimi a jihar nan,” A cewar sabon shugaban.

Kwamishinan hukumar na dindindin na daya, Alhaji Yakbu Barau Ningi, ya bayyana cewar dalibai da dama ne suka daukar darasi a jikin bijiyoyi wasu kuma a kasa babu kujerun zama, ya kuma ce makarantu da dama sun lalace wasu kuma rumfunansu ya yaye, don haka ne ya tabbatar da cewar za su yi dukkanin mai iyuwa wajen shawo kan matsalolin cikin kankanin lokaci.

Shi kuma sakataren dindindin na hukumar, Alhaji Abubakar Mansur ya bayar da tabbacin ma’aikatar hukumar na hada kai da sabon shugaban domin cimma nasarar tsare-tsaren da ya zo hukumar da su.

Malam Ahmad Muhammad Saka shine yayi magana a madadin iyalan sabon shugaban, ya fara da gode wa Allah a bisa samun babban mukami da dan uwansu yayi, kana ya kuma yi masa fatan kammala aiki lafiya, ya yi amfani da damar wajen jinjina wa kokarin gwamnan jihar Bauchi bisa wannan nadin da yayi wa dan uwansu, a cewarshi suna da tabbacin sabon shugaban zai bayar da gagarumar gudunmawa wajen kyautata harkar ilimi a jihar Bauchi.

Exit mobile version