Sabon Taki: Ma’aikatar Gona Ta Tarayya Ta Yi Bita Ga Manoman Kano

Ma`aikatar Gona ta Tarayya ta gudanar da bita ta musamman ga Manoman Jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkar Noma dangane da wani sabon ci gaba da aka samu a bangaren samar da wani sabon Takin Zamani, wanda ya fi dace wa da yanayin kasar nomanmu a halin yanzu tare da bunkasar samun amfanin Gona mai tarin yawan gaske kamar yadda sauran kasashen ke cin irin wannan moriya.

Injiniya Ohiare Badams John, shi ne Darakta mai kula da samar da kayayyakin aikin Gona daga Ma`aikatar Gona ta Tarayya, kazalika shi ne wanda ya jagoranci gabatar da wannan bita ga manoman na Jihar Kano. Haka nan, Daraktan ya cewa ya yi babban makasudun gabatar da wannan bita shi ne, don gabatar da wani sabon Takin zamani na Kamfanin NPK, wanda ya fi dacewa da zamani.

Injiniya ya ci gaba da cewa, buhun NPK daya kacal ya haura adadin buhu goma na gamagarin Takin Zamani na NPK wanda a da can baya ake amfani da shi. Saboda haka, wannan Taki na Zamani ko shakka babu shi ne ya fi dacewa da yanayin kasar da muke yin amfani da ita ta noma, sannan wannan kokari ne na Gwamanatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, na bunkasa aikin harkokin noma da kuma samar da wadataccen abinci a wannan kasa Nijeriya, ta yadda za ta iya dogara da kanta ba tare da ana ci gaba da shigo da shi daga kasashen waje ba, in ji Ohiare.

Haka zalika ya bayyana cewa, ko kadan wannan Taki ba shi da wata illa ga kasarmu ta noma, shi ne ma babban dalilin ya sa Ma`aikatar gona  ta Tarayyar Nijeriya, ta mike tsaye don kawo sauye-sauye da kuma bincike-bincike don ciyar da wannan kasa gaba.

A gefe guda kuma, shi ma Babban Jami`i mai kula da samar da Takin Zamani na Ma`aikatar aikin Gona ta Tarayya da ke Kano, Alhaji Bashir Abba Kasim cewa ya yi, akwai abubuwa da dama da aka lura da su dangane da gamagarin Takin da aka saba yin amfani da shi a baya. Don haka, yanzu a harkar da ta shafi noma kullum bincike ake yi ana sake kawo sabbin abubuwan da suka fi dacewa da kasar nomanmu.

Har ila yau, kafin zuwan wannan Taki sai da aka yi bincike aka tabbatar da cewa, kasar nomanmu ta yi daidai da sannan za a iya yin amfani da shi a duk fadin wannan kasa tamu Nijeriya. Haka nan, tuni aka yi kwakkwaren bincike tare da yin nazarin irin cututtukan da ke hana amfanin Gonarmu yin albarka.

Babu shakka, wannan sabon Taki da aka kawo, nan take zai kawar da ire-iren wadannan cututtuka ya kuma samar da albarkar Gona mai tarin yawa, wannan shi ne babban makasudin da ya sanya aka fitar da wannan Taki ta hanyar bincike irin Kimiyyar harkokin noma, wanda kuma a kullum gaba ake sake yi ba baya ba. Saboda haka, ya zama wajibi a rungumi wannan sabon Takin Zamani wanda tuni aka riga aka tabbatar da ingancinsa.

Har wa yau, Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa reshen Jihar Kano (AFAN), Alhaji Faruku Rabi`u Mudi, ya bayyana farin cikinsa da wannan bita da aka yi nasarar gudanawa a madadin sauran Manoman Jihar Kano. Kazalika, ya bayyanna gamsuwarsa da irin matakan da Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ke dauka wajen kokarin bunkasa harkokin Noman Rani da kuma na Damuna musamman ta hanyar bayar da basussuka da sauran tallafin noma a kowane lungu da sako na wannan kasa, a cewar tasa.

Exit mobile version