Dangane da bullo da sabon tsarinsa na ‘CBN Naira 4 Dollar Scheme’ wanda zai fara aiki a ranar Litinin, 8 ga Maris, 2021, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa, an dauki matakin ne da nufin samar wa ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje hanyoyi mafi sauki na aiko da kudade zuwa Nijeriya.
Gwamnan Babban bankin, Mista Godwin Emefiele ya bayyana hakan ne a karshen makon da ya gabata yayin gabatar da babban jawabi ga ‘Fagelity’s’s Inaugural Diaspora Webinar’ kan Illolin da tasirin sabon tsarin ‘FD Policy’ ya yi kan zuba jarin kasashen waje.
Mista Emefiele ya bayyana cewa, wannan matakin ya kuma kara fito da bayyane na shigo da kudade da rage ayyuka. Duk da cewa ya nuna kwarin gwiwarsa na cewa sabon tsarin zai karfafa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi wajen samar da kayayyaki da saka jari, wanda aka tsara domin jawo hannun jari daga ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.
Ya ci gaba da cewa, ana sa ran sabuwar manufar za ta fadada girman shigar da kudaden kasashen waje zuwa cikin kasar da nufin daidaita darajar canjin da kuma tallafawa samun dama ga ajiyar waje. Ya ce, mafi muhimmanci shi ne zai ba da dama ga ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje wajen saka jari a cikin kasarsu.
Da yake sake nanata samar da sabon zagayen, Gwamnan na CBN ya ce, Bankin ya gabatar da ragin Naira 5 ne a kan kowane Dala 1 na asusun da aka aika wa Nijeriya, ta hannun Jami’an cinikayyar kudi na duniya (IMTOs) da Babban Bankin ya ba da lasisi don zaburar da tsarin fitar da kudaden. Za a bayar da ragin ga asusun bankunan na wadanda suka ci gajiyar, biyo bayan samun kudaden shigar da aka yi.
Emefiele ya jaddada cewa, wannan sabon matakin zai taimaka matuka wajen ganin an tura kudi ta hanyoyin banki na yau da kullum cikin sauki ga ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje.
Da yake bayar da misali da shari’ar a wasu lokutan, Mista Emefiele ya ce, amfani da kudaden da aka sake biya na kudaden turawa ya kasance mai matukar muhimmanci wajen tallafawa ingantaccen shigar da kudaden zuwa kasashen da ke Kudancin Asiya da kuma inganta matsayinsu na biyan kudi, biyo bayan cutar korona.
Yayin da yake bayyana cewa matsakaicin kudin da ake turawa Nijeriya kudi ne daga Dala 200 zuwa Amurka, daga Amurka ya kai kimanin kaso 4.7, ya ce, bincike ya nuna cewa ko da an samu ragin kashi daya na kudin tura harajin hakan na iya haifar da matukar tasiri a shigo da kudaden.
“Kasashe a kudancin Asiya kamar Pakistan da Bangladesh suna sane da wannan tasirin kuma sun bullo da tsarin biyan kudin ne don tallafawa shigowa da kayayyaki. A Pakistan shirin wanda aka fi sani da aika sako ya ba da damar shigar da kudade sama da Dala Biliyan 2 a wata, ko da a lokacin cutar korona. Bangladesh kuma ta bullo da nata tsarin a watan Yunin 2019, wanda ya kasance kashi 2 cikin 100 na ragin shigar da kudi. Bayan wannan matakin, sun kuma ga an samu karin kaso 20 cikin dari na shigo da kudaden,” inji shi.
Da yake tsokaci kan batun zagaye-zagaye, kakakin Bankin da Ag, kuma daraktan sashin sadarwa na Kamfanin, Osita Nwanisobi ya bayyana cewa, akwai iyakar adadin da za a iya aikawa ta IMTO, kuma babu wani abokin ciniki da zai iya aika Dala 100,000 ta hanyar IMTO.
Duk da cewa ya amince da cewa matakin na CBN bai kai yadda ya kamata ba wajen bayar da kudaden gaba daya, Nwanisobi ya ce, wannan mataki ne na tafiya kan turbar da ta dace wajen rage wahalhalun kudin da ‘yan Nijeriya ke kashewa wajen turawa Nijeriya kudade.
Yayinda yake kuma bayyana cewa, da kasancewar kalubale na farko na hadewar hanyar sadarwa, Nwanisobi Emefiele ya tabbatar da cewa CBN zai ci gaba da aiki kai tsaye don magance ‘yan kalubalen da suka rage.